Babban bankin Najeriya ya fadi adadin kudin jabun da aka gano a shekarar da ta wuce
Babban bankin Najeriya wanda aka fi sani da Central Bank of Nigeria wato CBN ya ce a shekarar 2018 an gano kudaden jabun da yawansu ya kai naira miliyan 98.82.
Bankin ya fitar da wannan labarin ne a cikin rahoton kudi na shekarar 2018 wanda ya wallafa a shafinsa na yanar gizo.
KU KARANTA:Gwamnan Nasarawa ya mika sunayen zababbun kwamshinoni guda 15 ga Majalisar jihar
Bankin ya ce wannan kididdigar ta kudaden jabun ta ragu da kashi 1.30% da kuma kari ta wani bangare da kashi 5.77% fiye da yadda yake a shekarar 2017.
Kididdigar waccan lokacin ta nuna cewa yadda takardun kudin ke yawo a kasar nan ya karu daga 16 zuwa 18. Haka kuma a cikin rahoton bankin ya fadi cewa naira 1000 da naira 500 su ne wadanda aka fi yin jabunsu a Najeriya.
Bankin na cigaba da cewa, domin magance wannan matsalar ta buga jabun kudi, za a iya amfani da jami’an tsaron, sauran bankuna da kuma wuraren ajiya na musamman a Najeriya.
Bankin CBN ya kara da cewa an samu kari a bangaren kudin da ake kashewa yau da kullum inda ya karu da kashi 0.8% a lissafin naira kuwa ya kama biliyan N2,3297 a karshen Disemban 2018.
A wani labarin mai kama da wannan za ku ji cewa, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya nada sabon shugaban ma’aikatansa bayan da Edward Onoja yayi murabus domin tsayawa takarar mataimakin gwamnan jihar.
Abdulkareem Jami’u shi ne wanda aka nada mukamin, kuma kamar yadda sakatariyar Gwamnan Kogi, Mrs Folashade ta bayar da sanarwar cewa nadin nasu ya fara aikin ne tun ranar Litinin 14 ga watan Oktoba.
https://punchng.com/n98-82m-fake-banknotes-detected-in-2018-cbn/amp/?__twitter_impression=true
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng