Gwamnan Nasarawa ya mika sunayen zababbun kwamshinoni guda 15 ga Majalisar jihar

Gwamnan Nasarawa ya mika sunayen zababbun kwamshinoni guda 15 ga Majalisar jihar

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a ranar Laraba 16 ga watan Oktoba, 2019 ya mika sunayen zababbun kwamishinoninsa guda 15 ga majalisar dokoki domin a tantancesu.

Kakakin majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi ne ya sanar da wannan magana ga majalisar bayan da Shugaban masu rinjayen majalisar ya soma gabatar da sunayen.

KU KARANTA:Ana daf da zaben Kogi, Yahaya Bello yayi nadin sabon mukami

Ga jerin sunayen kwamishinonin 15 kamar haka: Ahmed Baba Yahaya (Karamar hukumar Toto), Philip Dada (Karu), Othman Bala Adam (Keffi), Dr Abdulkarim Abubakar Kana (Kokona), Obadiah Boyi (Akwanga), Yusuf Aliyu Turaki (Awe), Dr Salihu Ahmad Alizaga (Nasarawa Eggon).

Sauran kuwa sun hada da; Dogo Shammah (Wamba), Otaki Allahnanah (Keana), Haruna Ogbole Adamu (Obi), Ibrahim Musa Ekye (Doma), Mrs Fati Jimeta Sabo (Nasarawa), Abubakar Muhammad Imam (Lafia), Halima Ahmadu Jabiru (Lafia) da Mohammed Bashir Aliyu (Lafia).

Kakakakin majalisar, Ibrahim Balarabe ya umarci kwamishinonin da su kawo takardunsu na CV guda talatin-talatin daga yau zuwa 18 ga watan Oktoba.

Balarabe ya ce: “Majalisa za ta soma tantance kwamishinonin a ranar Litinin 21 ga watan Oktoba, kuma za a fara ne daga karamar hukumar Toto, Karu, Keffi, Kokona, Akwanga, Awe, Nassarawa Eggon, Wamba da Keana.

“Sauran kuma kanan hukumomin da za a tantance ranar Talata 22 ga watan Oktoba, 2019 sun hada da; Obi, Doma, Nasarawa da kuma mutane uku daga Lafia.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel