Ilimin kimiyya zai magance matsalolin nahiyar Afirka, inji Gwamnan APC

Ilimin kimiyya zai magance matsalolin nahiyar Afirka, inji Gwamnan APC

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ce amfani da ilimin kimiyya ta hanyar da ya dace zai magance matsalolin da nahiyar Afirka ke fama da su.

Gwamnan ya ce shi a karon kansa da sauran shuwagabanni a Najeriya na iya baki kokarinsu ganin cewa an inganta makarantu musamman sashe koyar da ilimin kimiyya.

KU KARANTA:Gwamna Bello ya ware biliyoyin kudi domin yin aikin tituna a jihar Neja

Buni ya fadi wannan maganar ne ranar Litinin 14 ga watan Oktoba a Abuja wurin wani taron karawa juna sani game da kimiyya, sadarwa da kuma aikin jarida.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin Barrister Ahmed Mustapha, mai ba shi shawara a kan lamuran shari’a ya ce, a jiharsa ya riga da sanya ilimi a karkashin dokar karta-kwana domin daga martabar ilimi musamman na kimiyya a jihar Yobe.

Mai Mala Buni wanda shi ne shugaban taron ya ce: “Ina matukar farin ciki da kasancewa shugaban wannan taro wanda ke cike da kwararru a fanni kimiyya da kuma aikin jarida.

“Jihohi da dama a Najeriya na kokarin ganin sun yi gyara a fanni ilimi, jihar Yobe na daya daga cikinsu. A halin yanzu a jihar Yobe ilimi na karkashin dokar karta-kwana ne. Bangaren kimiyya da kere-kere su ne muka fi mayar da hankali a kansu.” Inji Gwamnan.

Daya daga cikin manyan bakin da suka halarci taron, Mahmood Bukar Maina ya ce, daga cikin matsalolin da kimiyya ke fuskanta akwai al’adu da kuma addini a wasu wuraren, amma dai da tsari mai kyau Najeriya za ta inganta ta hanyar kimiyya.

https://leadership.ng/2019/10/16/sciencell-solve-africa-challenges-says-yobe-gov/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel