Aso rock: Ku binciki hakikanin abinda ke faruwa a Villa, PDP tayi kira ga Majalisar dokoki

Aso rock: Ku binciki hakikanin abinda ke faruwa a Villa, PDP tayi kira ga Majalisar dokoki

Jam’iyyar adawa ta PDP tayi kira ga Majalisar dokokin Najeriya inda ta nemi ta gudanar da bincike game da irin wainar da ake toyawa a cikin Fadr Shugaban kasa ta Villa.

A cikin wani zancen da sakataren jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Talata 15 ga watan Oktoba, 2019, ya yi magana kan cewa akwai al’amuran rashin gaskiya da dama dake aukuwa a cikin fadar ta Villa.

KU KARANTA:Operation Python Dance: An bai wa daruruwan sojoji horo a jihar Imo domin su kula da yankin Igbo

Kamar yadda jam’iyyar ke fadi, ta ce Buhari ya baiwa wadansu mutane ofis duk da cewa ba su rike da ko wane mukami a gwamnatinsa. Akwai zargin cin-hanci da rashawa a tattare da Fadar Shugaban kasan, a cewar PDP.

Haka kuma, PDP ta bayyana rikicin Aisha Buhari da diyar Mamman Daura a kan daki, a matsayin wani abin kunya babba. Wannan rikicin ya sanya mutane suka san cewa akwai rikita-rikita a fadar Shugaban kasan.

Kola ya ce: “Yanzu ‘yan Najeyiya za su iya ganin dalilin da ya hana kasarmu samun ingantaccen jagoranci karkashin Shugabancin Buhari. Jam’iyyarmu ta san cewa kasarmu na cikin halin kunci a karkashin mulkin APC da Shugaba Buhari.

“A don haka PDP na kira ga Shugaba Buhari cewa yayi gaggawar neman afuwar ‘yan Najeriya bisa halin da ya jefa kasar nan a ciki. Kuma yayi shirin barin ofishin Shugaban kasa domin wanda yafi shi cancanta yazo yah au.

“Haka kuma muna kira ‘yan Najeriya da su kara hakuri da juriya kasancewar wannan mulki mai cike da rashin cigaba da kunci ya kusa zuwa karshe, a Kotun koli za a karkare komi.” Inji PDP.

https://www.dailytrust.com.ng/probe-illegality-in-presidential-villa-pdp-asks-national-assembly.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel