Tambuwal ya bada filin ginin sabuwar Jami’a a Sokoto

Tambuwal ya bada filin ginin sabuwar Jami’a a Sokoto

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya umarci ma’aikatar filaye da gidaje ta jihar Sokoto da ta fitar da fili na musamman domin ginin Jami’ar Nana Asma’u ta karatun kimiyyar kiwon lafiya.

Gidauniyar Mai-alfarma Sarkin Musulmi ne za ta gina jami’ar. Tambuwal ya bada wannan umarnin ne a ranar Litinin 14 ga watan Oktoba, a lokain da yake karbar wadansu littatafan da gidauniyar ta wallafa na Shehu Usmanu Danfodiyo, Abdullahi Gwandu da kuma Sarkin Musulmi Muhammadu Bello.

KU KARANTA:Jita-jitar auren Buhari: Sarkin Gwandu ya yi kira ga kafafen yada labarai da su rinka nuna gogewa a aikinsu

Gwamnan ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da taimakawa ilimin ‘ya’ya mata a jihar tun daga matakin firamare har zuwa jami’a.

Haka kuma, ya bayyana aniyar gwamnatinsa na cigaba da fitowa da ayyukan da daular Shehu Danfodiyo tayi a Sokoto tun daga lokacin da aka kafata har izuwa yau.

Tambuwal ya jinjinawa Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Muhammadu Mera a madadin shuwagabannin daular ta Usmaniyya saboda irin gudunmuwar da ya bada wurin ganin an samu nasarar wallafa littafan.

Ya kuma kara da cewa, daular ta jima da nata salon jagoranci tun gabanin zuwan turawa yamma kasar hausa, hakan nema ya sanya daular ta kasance abin koyi.

A nasa jawabin kuwa, Sarkin Gwandu wanda shi ne ya jagoranci buga littafan ya yabawa gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal bisa daukar nauyin buga littafan guda 92 da tayi.

Ya kuma kara da yi masa addu’ar Allah ya saka masa da alkhairinsa. Alhaji Muhammadu Mera ya ce an rarraba littafan zuwa makarantu daban-daban kama da wadanda ken an Najeriya da kuma kasashen waje kamar irinsu Amurka da Dubai.

https://tribuneonlineng.com/tambuwal-allocates-land-for-proposed-nana-asmau-university-in-sokoto/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel