Tirkashi: An kama wani fasto da ya yiwa mambobin cocin shi sama da 20 cikin shege

Tirkashi: An kama wani fasto da ya yiwa mambobin cocin shi sama da 20 cikin shege

- Wani fasto da ya kware wajen yiwa mambobin shi cikin shege ya shiga hannun jami'an 'yan sanda

- An kama faston ya yiwa sama da mata guda ashirin cikin shege, ciki kuwa hadda masu aure da 'yammata

An kama wani fasto mai shekaru 53 da ya yiwa mambobin cocin shi sama da guda ashirin cikin shege, ciki kuwa hadda matan aure da 'yammata kanana, inda ya bayyana cewa an umarce shi da yayi zina da su ne.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Enugu, DSP Ebere Amaraizu, ya bayyana cewa sun kama Fasto Timothy Ngwu da laifin yiwa mambobin cocinsa mata cikin shege.

Kakakin rundunar ya ce: "A duk lokacin da mace ta haifi jariri, jaririn da mahaifiyarsa za suyi ta zama a cikin cocin har karshen rayuwarsu," ya kara da cewa matar Faston ce ta kai karar shi akan abinda yake yi.

Matar mai suna Veronica Ngwu, wacce ta gaji da halayyar mijinta bayan ya yiwa 'yar kanin shi ciki, wanda ya nuna a saye sunan shi, ya bayyana cewa ya jima yana gargadin Fasto din da da iyalan shi akan halayyar da yake yi marar kyau, amma sunki su saurare shi.

KU KARANTA: Ana wata ga wata: Hadiza Gabon ta sanya baki a rigimar Sadiya Haruna da Isah A Isah, bayan ta kirashi da dan luwadi

"Masifar Allah ce ta fadowa dan uwana, mun sha gargadin shi akan ya daina abinda yake yi, amma yaki yadda. Har zargin mu yake yi da muna yi masa bakin ciki da abinda yake yi saboda munga yana yin aikin Allah."

"Ya saki matar shi ta sunna wacce suke da yara guda uku, ya koma yiwa matan aure da yammata cikin shege, kalli cikin gidan nan yadda ya cika shi da yara," in ji shi, "daga yaya mutum mai ilimi irinshi ya dinga yin abu irin na jahilai?"

Dan uwan nashi ya kara da cewa Ngwu yana da kimanin mata guda 5 da 'ya'ya guda 13 da kwarkwara wanda ya bayyana cewa ubangijin shi ne yace ya aura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: