Jita-jitar auren Buhari: Sarkin Gwandu ya yi kira ga kafafen yada labarai da su rinka nuna gogewa a aikinsu

Jita-jitar auren Buhari: Sarkin Gwandu ya yi kira ga kafafen yada labarai da su rinka nuna gogewa a aikinsu

-Sarkin Gwandu ya gargadi masu kafafen yada labarai a kan illar yada jita-jita

-Sarki Muhammadu Bashar ya yi wannan maganar ne ranar Talata a Birnin Kebbi

-Muhammadu Bashar ya ce abin kunya ne kafafen yada labaran Najeriya suka yi na kirkirar aure su daurawa Shugaban kasa ba tare da saninsa ba

Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Basar yayi kira ga kafafen yada labarai da su rinka nuna gogewa da kwarewar aiki kafin su fitar da labarai ga ‘yan Najeriya.

Sarkin ya bada wannan shawarar ne a lokacin da yake janyo hankalin masu da tsaki a kan lamuran yada labarai, ranar Talata 15 ga watan Oktoba, 2019 a Birnin Kebbi.

KU KARANTA:Babu yunwa a kasar nan, Najeriya na noma abinda za ta iya ciyar da kanta – Nanono

Sarkin ya ce: “Lalacewarmu har ta kai matakin da zamu iya yiwa Shugaban kasar mu karya kuma kafafen yada labarai su watsa ta duniya ta gani.

“Kafafen yada labarai suka yi ta yada wannan labarin game da auren Shugaba Muhammadu, tare da fadin wurin da za a daura auren, rana da kuma lokaci ba tare da shi kansa ma ya san da maganar ba.” Inji Sarki Muhammadu Bashar.

Muhammadu Bashar ya kara da cewa, ba karamin abin kunya bane ‘yan Najeriya suka yiwa shugaban kasa saboda an kirkiri karya an jingina masa.

“Ya kamata kafafen yada labarai su rinka lura da abinda suke yadawa zuwa ga duniya. Akwai dokoki na aikinsu, haka kuma akwai abubuwa da dokar ta hana su yi don haka sai a kiyaye.” Inji Sarkin.

A karshe Sarkin ya gargadi masu kafafen yada labaran da su lura sosai wurin yada labarai marasa tushe, kuma su tuna hukunci yada labaran karya a addini, saboda haka su ji tsoron Allah su guji irin wannan aiki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel