Yan Najeriya miliyan 15 ne suke fafutukar neman aikin yi a Najeriya – Gwamnati

Yan Najeriya miliyan 15 ne suke fafutukar neman aikin yi a Najeriya – Gwamnati

Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwarta game da hauhawar adadin yan Najeriya dake neman aikin yi, musamman ma manyan ayyuka masu gwaggwaban albashi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ministan kwadago, Chris Ngige ne ya bayyana wannan damuwar a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Enugu na jahar Enugu.

KU KARANTA: Gwamnatin Neja ta rufe makarantu guda 2000 marasa inganci a Suleja

A jawabinsa, Ngige yace: “Matsalar rashin aikin yi a tsakanin ma’aikata na cigaba da zama babbar kalubale ga gwamnatin Najeriya, wanda shine ummul haba’isun karuwar aikata miyakun laifuka, don haka lamarin na damun gwamnati.

“Idan har bamu magance matsalar ba, zamu wayi gari wata rana kasar gaba daya ta tsunduma cikin tashin tashina tsundum, alamomin matsalar rashin aikin yi sun hada da Boko Haram, IPOB, tare da bacin rai da kuma shiga halin damuwa da mutane suke yi.

“Haka zalika ayyukan yan bindiga a Arewacin Najeriya, garkuwa da mutane da ake samu a dukkanin sassan kasar nan na daga cikin illolin rashin ayyukan yi ga matasa, kamar yadda kungiyar tsagerun Avengers yake, su OPC, duk hadasu a ciki.” Inji shi.

A cigaba da jawabinsa, Ngige yace gwamnati za ta cigaba da samar da hanyoyin rage radadin rashin aikin yi, ya kara da cewa ko a yanzu gwamnati na iya bakin kokarinta, amma dai matakan da suke dauka basu isa bane.

“Mun kirkiri hanyoyin tallafa ma manoma, kuma an samu nasara sakamakon mutane da dama sun koma gona, mun samar da tsarin N-Power inda muka dauki matasa 500,000 aikin amma dai ya yi kadan, amma akwai masu neman gwaggwaban aikin yi kusan miliyan 15.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel