‘Yan sanda sun yiwa wani lauya dukan a kawo wuka a Anambra har sai da ya suma

‘Yan sanda sun yiwa wani lauya dukan a kawo wuka a Anambra har sai da ya suma

Wani lauya mazaunin garin Onitsha mai suna Jacob Obasi ya suma a sakamakon dukan a kawo wuka da wasu jami’an ‘yan sandan Anambra su kayi masa ranar Asabar 12 ga watan Oktoba.

Wani wanda ya kwaci lauyan a hannun ‘yan sandan yayi gaggawar kai shi asibiti, yayin da ya abin ya auku a kan idonsa lokacin da hanya ta biyo da shi wurin.

KU KARANTA:Boko Haram: Buhari zai nemi gudunmuwar sojoji daga wurin Shugaban Rasha, Putin

Jaridar Punch ta tattaro mana bayanin cewa, laifin lauyan guda daya ne kacal kuma shi ne kokarin da yayi na shiga tsakanin ‘yan sandan da wani mutum a unguwarsu.

Kungiyar lauyoyin Najeriya wato NBA, tayi Allah wadan irin wannan aiki, inda ta ce ko kadan abinda ‘yan sandan su kayi ba su kyauta ba kuma ba su mutunta aikinsu ba.

A cikin wani zancen da shugaban NBA reshen jihar Onitsha ya fitar game da lamarin, Ozoemena Erinne ya ce kungiyarsu ta dauki matakin ganin cewa hukumar ‘yan sanda ta hukunta jami’an da suka aikata wannan danyen aiki.

Ga abinda zancen ke fadi: “Kungiyarmu ta samu labarin cewa laifin Jacob Obasi shi ne kawai na shiga tsakanin ‘yan sandan da wani mutum da ‘yan sandan ke muzugunawa a unguwarsu.

“A kokarinsa na ceto wannan bawan Allan daga gana masa azaba da ‘yan sandan ke yi shi ne kadai laifinsa. Hakan ya harzukasu suka lakada masa dukan tsiya har da buga masa kan bindiga.

“A sakamakon wannan dukan, Obasi ya samu munanan raunuka, yanzu haka yana kwance a Babban Asibitin Onitsha inda yake karbar magani.” Inji Kungiyar.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan Anambra, Haruna Mohammed ya bayyana rashin jin dadinsa bisa aukuwar wannan abu, amma ya bamu tabbacin cewa hukumar ‘yan sanda za ta bincike lamarin a karkashin umarnin kwamishinan ‘yan sandan jihar.

https://punchng.com/police-beat-anambra-lawyer-to-coma/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel