Boko Haram: Buhari zai nemi gudunmuwar sojoji daga wurin Shugaban Rasha, Putin

Boko Haram: Buhari zai nemi gudunmuwar sojoji daga wurin Shugaban Rasha, Putin

Jakadan Najeriya a kasar Rasha wanda ke birnin Moscow ya ce, Shugaba Muhammadu Buhari yana da shirin rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar da za ta samawa Najeriya karin sojoji daga wurin Shugaba Vladimir Putin.

Haka zalika, mun samu labarin cewa Shugaban kasar Najeriya zai gamu ne da Putin a wurin taron Afirka da Rusha wanda za a gudanar a birnin Sochi, kasancewar kasar Rasha na son ta fadada alakarta da Afirka.

KU KARANTA:Bidiyo: Indai Smart ne ba tun yau na saba kada shi a zabe ba, inji Dino Melaye

“Muna da tabbacin cewa da taimakon kasar Rasha zamu iya ganin bayan Boko Haram, duba ga irin kwarewar sojojinsu wurin yakar ISIS a kasar Syria.” Inji jakadan, Steve Ugbah.

Ya kuma kara da cewa, Najeriya na da niyyar sayen helikwata, jiragen yaki da kuma igwa daga hannun kasar Rasha. An riga da tsara yarjejeniyar a rubuce tsakanin Najeriya da Rasha domin samun karin karfin sojoji, a cewar jakadan.

“Muna fatan Shugaba Buhari zai iya baki kokarinsa na ganin an cinma wannan manufar. Yarjejeniyar idan aka kullata za ta bude wasu hanyoyi musamman na bayar da horo da kuma karin kayan aiki ga sojojin Najeriya.” Inji Steve.

A wani labarin kuwa zaku ji cewa, Sanata Dino Melaye ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na facebook inda yake cewa: “Ba tun yau na saba kayar da Adeyemi a zabe ba, nayi na daya nayi na biyu yanzu na uku muke hari kuma ni zan lashe.”

Dino ya fitar da wannan bidiyon ne bayan Kotun daukaka kara a jiya Juma’a 11 ga watan Oktoba ta soke zabensa, inda tab a INEC umarnin a sake yin sabo.

https://tribuneonlineng.com/boko-haram-buhari-to-sign-military-cooperation-deal-with-putin-in-russia/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel