Neymar ya kafa wani babban tarihi a wasan kwallon kafan Brazil

Neymar ya kafa wani babban tarihi a wasan kwallon kafan Brazil

Dan wasan kwallon kafan Brazil da PSG na kasar Faransa, ya kafa tarihi a kasarsa ta Brazil inda ya zamo dan wasa mafi karancin shekaru da ya bugawa kasar Brazil wasanni 100.

Sai dai kuma duk da wannan tarihin da dan wasan ya kafa a ranar Alhamis, kasarsa ta Brazil ta tashi kunnen doki da ci 1-1 a wani wasan sada zumunta tsakaninsu da Senegal. Inda dan wasan ya gagara jefa kwallo a raga.

KU KARANTA:Gwamnatin tarayya da kamfanin CRCC na China za su shimfida layin dogo na $3.9bn daga Abuja zuwa Itakpe

Dan wasan gaban Liverpool, Roberto Firmino ne ya fara zura kwallon farko a raga ana minti takwas kacal da soma wasan bayan Coutinho ya tsige masa wata kwallo mai kyau.

Haka aka cigaba da gwabzawa tsakanin kasashen biyu inda kyaftin Senegal Cheikhou Kouyate ya ja ragamar kasarsa wurin kaiwa Brazil kora a lokuta da dama.

Famara Diedhiou na kasar Senegal ne ya ramo kwallon da aka ci kasarsu a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan an kayar da Sadio Mane a cikin akwati.

Neymar ya samu wani bugun tazara a minti 67 inda ya buga kwallon da kyau sai dai ta tashi sama kadan daga inda raga take.

Har wa yau, duk da Neymar bai samu ya zura kwallo ko daya ba a raga har aka tashi wasan sada zumuntan. Babbar rana ce a gare shi saboda ya kafa tarihi kasancewarsa dan shekaru 27 na farko da ya fara bugawa Brazil wasanni har 100.

A cikin wasanni da ya bugawa Brazil ya samu damar zura kwallaye 61 a raga inda yake mataki a jerin ‘yan wasan da suka fi kowa zura kwallaye a Brazil, Pele ne na daya sai Ronaldo a mataki na biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel