Yara 102,000 ke mutuwa duk shekara sakamakon rashin tsaftar muhalli – Minista

Yara 102,000 ke mutuwa duk shekara sakamakon rashin tsaftar muhalli – Minista

Kimanin yara ‘yan kasa da shekara biyar 102,000 ke mutuwa a ko wace shekara sakamakon cututtuka da ake samu daga muhalli mara tsafta, inji Minista albarkatun ruwa, Engr Suleiman H. Adamu.

Ministan wanda ya fadi wannan maganar a wata hira da ‘yan jarida, gabanin ranar wanke hannu ta duniya ya ce, kimanin 33% na yara ‘yan kasa da shekara biyar na fama da rashin samun abinci mai gina jiki.

KU KARANTA:Taraba: Mun samu matsalolin satar mutane har guda 100 a cikin wata 9 – Gwamna Ishaku

Jaridar Daily Trust ta kawo mana rahoton cewa, ranar wanke hannu ta duniya ana bikinta a ko wace ranar 15 ga watan Oktoba, kamar yadda majalisar dinkin duniya ta sanya ranar.

Kuma an zabi ranar ne domin tunatar da mutane a kan muhimmancin tsaftace hannayensu musamman ta hanyar amfani da sabulun wanke hannun.

Ministan ya bayyana hanyar wanke hannun a matsayi abu mai sauki ta yadda kowa zai iya yi domin kula da lafiyarsa. Tsaftar hannayen tamkar rigakafi ce daga cutar gudawa, amai da zawo, zazzabin typhoid da kuma nimoniya.

Adamu ya ce: “Wanke hannu yana rage mutuwar yara ta hanyar tsare aukuwar cutar amai da zawo. Haka kuma yana kare aukuwar cututtuka da dama wadanda ke kisa kai tsaye.”

Ministan yayi korafi game da rashin samar da sabulun wanke hannuwa a makarantu, inda ya ce akwai bukatar a ce makarantu su mallake shi domin tabbatar da an tsare yaran daga cututtuka daban-daban da rashinsa kan iya haifarwa.

https://www.dailytrust.com.ng/102000-children-die-of-poor-sanitation-yearly-minister.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel