NYSC ta kama mutum 95 da takardun makaranta na bogi

NYSC ta kama mutum 95 da takardun makaranta na bogi

Darakta janar na NYSC, Birgediya janar Shuaibu Ibrahim ya ce kimanin mutum 95 ne aka kama da takardun makaranta na karya a yayin bayar da horo ga daliban da suka kammala karatun jami’a na NYSC a bara.

Kamar yadda shugaban hukumar na NYSC ya fadi wasu daga cikin mutanen na dauke ne da takardun makarantun kasashen waje yayin da sauran kuwa ke dauke da takardun makarantun Najeriya.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta soma muhawara a kan kasafin kudin 2020

Tuni hukumar NYSC ta mika wadannan mutanen zuwa ga hannun hukumomin tsaro domin su fuskanci hukunci daidai da su.

Da yake magana a Minna babban birnin jihar Neja ranar Laraba 9 ga watan Oktoba, 2019 wurin taron wayar da kai game da sansanin horar da masu yiwa kasa hidima rukunin C na shekarar 2019, Ibrahim ya ce, 50 daga cikin daliban na dauke ne da takardun jami’o’in Najeriya yayin da 30 ke dauke da takardun jami’o’in kasashen yammacin Afirka.

Shugaban ya kara da cewa, “wadansu daga cikin jami’o’in Najeriya na sayarwa wadanda ba dalibansu bad a takardar shaidan kammala karatu domin kawai su samu damar yin bautar kasa na NYSC.”

Shugaban yayi Allah tir da irin wannan danyen aikin, inda yake cewa ire-iren wadannan ayyuka ne ke kawo lalata suna da kuma koma bayan hukumar ta NYSC. Haka kuma yana iya haifar da matsaloli daban-daban a bangaren cigaban kasa.

A karshe Ibrahim ya ce ba zai bata lokaci ba wurin fallasa sunayen jami’o’in da wannan laifin ya shafa a jaridu domin duniya ta san abinda suke ciki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel