‘Yan bindiga sun kashe mata 3 a Barikin Ladin jihar Filato

‘Yan bindiga sun kashe mata 3 a Barikin Ladin jihar Filato

Mun samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe mata uku ta hanyar harbin bindiga a unguwar Vatt dake cikin karamar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato.

Wani shugaban kungiyar matasan yankin, Dalyop Solomon ne ya bada wannan labarin jiya Talata a Jos inda ya ce, al’amarin dai ya auku ne a yammancin Litinin yayin da mata ke girbar tumatur a wata gona.

KU KARANTA:Bauchi: Jam’iyyar APC za ta daukaka kara game da zaben Gwamnan jihar

Solomon ya fadi sunayen matan da wannan iftala’i ya afaka ma kamar haka, Tabitha Dung, Ngo Yop Gwom Pam da Zong inda ya kara da cewa an mika gawarwakinsu zuwa dakin ajiyar gawa na asibitin garinsu.

Solomon ya ce: “Mutanenmu na zaman makoki a yanzu haka, saboda ‘yan bindiga da muke zargin Fulani makiyaya ne suka shiga wata gona dake shiyyar Foron a garin Vatt suka kashe mata 3.

“Wannan aika-aika ne ya yi sanadiyar mutuwar Tabitha Joro Dung, Ngo Yop Gwom Pam da Zong Peter sakamakon harbinsu da makiyayan suka yi. An riga da an kai gawarwakinsu zuwa dakin ajiyar gawa na asibiti wato mucuware.”

Ya kuma kara da cewa, jami’an tsaro sun ziyarci wurin da wannan abu ya faru kuma sun dau alkawarin zakulo wadanda suka aikata wannan ta’adi tare da hukuntasu kamar yadda shari’a ta tanada.

A wani labarin kuwa, zaku ji cewa jam'iyyar APC a jihar Bauchi ta ce za ta daukaka kara zuwa kotu ta gaba, bayan kotun zaben tayi watsi da kararta inda take kalubalantar nasarar Gwamna Bala Mohammed.

Shugaban APC na jihar Bauchi, Uba Bana ne ya bada wannan sanarwar inda ya ce sun riga da sun kammala shirye-shiryen daukaka karar.

https://www.thisdaylive.com/index.php/2019/10/09/bandits-kill-three-women-in-plateau-village/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel