Bauchi: Jam’iyyar APC za ta daukaka kara game da zaben Gwamnan jihar

Bauchi: Jam’iyyar APC za ta daukaka kara game da zaben Gwamnan jihar

Jam’iyyar APC ta ce za ta daukaka kara zuwa kotun gaba bayan da kotun zaben Gwamnan jihar Bauchi tayi watsi da kararta wadda take kalubalantar nasarar Bala Mohammed na PDP.

Uba Nana, shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi ne ya bayar da sanarwar ranar Talata 8 ga watan Oktoba a lokacin da yake zantawa da manema labarai.

KU KARANTA:Rufe kan iyaka: Duk da samun N5bn a ko wace rana, jami’an kwastam sun koka akan rashin samun alawus

Ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da cewa ka das u karaya kuma sun kwantar da hankalinsu a kan abinda ya faru a kotun zabe saboda za su daukaka kara zuwa kotu ta gaba.

“Mu mutane ne masu kaunar zaman lafiya da kwanciyar hankali, muna kuma mutunta shari’a da hukuncin da kotu ta yanke. Amma dai ba za muyi kasa a gwiwa ba wajen ganin mun bi hanyoyin shari’a domin dawo da mulki hannunmu wanda aka rabamu da shi.” Inji Nana.

Idan baku manta ba dai a ranar Litinin 7 ga watan Oktoba ne kotun zabe ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed na PDP inda tayi watsi da karar APC da kuma dan takararta tsohon gwamnan jihar Mohammed Abubakar.

Kotun tayi watsi da karar da ne kasancewar masu karar sun gagara gabatar da hujjoji gamsassu game da magudin da suke ikirarin cewa an tafka a wadansu rumfunan zabe dake kananan hukumomin Tafawa Balewa da Bogoro na jihar Bauchi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel