Matashi dan shekara 21 ya bayyana a gaban kotu bayan an kama shi da bindiga

Matashi dan shekara 21 ya bayyana a gaban kotu bayan an kama shi da bindiga

Wani matashi mai suna Ahmed Lukman ya bayyana a gaban wata Kotun Majistare dake Ikeja ranar Talata 8 ga watan Oktoba a sakamakon kama shi da akayi dauke da bindiga.

Lukman wanda ya ce sana’ar walda ce aikinsa yana zaune a gida mai lamba 5 titin Ikosile dake Ijora a unguwar Badia ta jihar Legas.

KU KARANTA:Kudin makamai : Kotu ta sanya ranar da za ta cigaba da shari'a tsakanin EFCC da Dasuki

Sajan Chekube Okeh wanda shi ne ya shigar da karar ya shaidawa kotu cewa a ranar 14 ga watan Satumba aka kama Lukman a tsakanin Amukoko da Ijora a cikin Legas.

Okeh ya bayyana mana cewa, jami’an ‘yan sandan dake aikin kaiwa da komowa a tsakanin hanyar ne suka hangi Lukman kana suka kai masa farmaki kasancewar alamun sun tabbatar masu da cewa ba shi da gaskiya.

Bayan sun isa wurin da yake, sai suka caje shi inda aka same shi dauke da bindiga kirar dobul barel irin ta gargajiya a cikin aljihunsa, a cewar Okeh.

“Akwai wani kwankon harsashi da aka samu tare da shi, inda aka tambaye shi jawabi game da harsashin amma ya gaza, a don haka aka kama shi.” Inji Okeh.

Laifin da Lukman ya aikata ya ci karo da sashe na 1 da kuma na 411 a cikin kundin dokokin miyagun laifuka na jihar Legas, 2015.

Sai dai kuma wanda ake tuhumar ya ki amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa. Mai shari’ar kotun, Mrs A.O Akinde ta bayar da belin Lukman a kan naira N500,000 tare kuma da dage karar zuwa 21 ga watan Oktoba.

https://www.vanguardngr.com/2019/10/man-21-in-court-over-alleged-possession-of-gun/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel