Zargin cin-hanci: Mu hadu a kotu, tsohon gwamnan jihar Bauchi ya maka gwamnatin jihar kara

Zargin cin-hanci: Mu hadu a kotu, tsohon gwamnan jihar Bauchi ya maka gwamnatin jihar kara

Tsohon gwamnan jihar Bauchi ya ci alwashin kai karar gwamnatin Jihar Bauchi zuwa kotu bisa rahoton da wani kwamitin gwamnatin ya fitar me cewa ana zarginsa da baddakalar wadansu kudade.

A cikin wani zance da ya samu sanya hannun hadimin tsohon gwamnan, Ali M. Ali jiya Asabar 5 ga watan Oktoba a Bauchi ya ce, tsohon gwamnan zai dauki matakin shari’a a kan kazafin da akayi masa na cewa ya wawure wasu kudade.

KU KARANTA:Gwamna Yahaya ya dau aniyar ganin bayan matsalar wutar lantarki a Gombe

Kwamitin bincike da kuma dawo da kudaden gwamnatin da ake sace na Bauchi ne ya fitar da wani jawabi ranar Laraba 3 ga watan Oktoba inda ya ayyana gwamna Abubakar da cewa yak eta dokokin kula da wasu kudade mallakar gwamnatin jihar Bauchi a lokacin mulkinsa.

Mai magana da yawun bakin kwamitin, Umar Barau Ningi wanda ya karanto jawabin ga manema labarai ya ce sun samu abubuwa da dama daga cikin bincikensu wadanda suka shafi, handama, sata da kuma zunzurutun son kai tare da keta dokar ofis.

A cewarsa, tsohon gwamnan ya sayarwa kansa da motoci guda bakwai ba tare da la’akari da dokokin gwamnatin jihar Bauchi ba, saboda kafin a samu amincewar irin wannan abu dole sai da yarjejeniya wadda ta yi daidai da dokokin BMPIPP na shekarar 2008 na gwamnatin jihar Bauchi.

https://www.dailytrust.com.ng/well-meet-in-court-to-prove-corruption-allegation-bauchi-ex-gov-tells-incumbent.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel