Ka rage albashin sanatoci da 'yan majalisr wakilai domin samawa 'yan Najeriya aikin yi, sakon Sarki Sanusi zuwa ga Buhari

Ka rage albashin sanatoci da 'yan majalisr wakilai domin samawa 'yan Najeriya aikin yi, sakon Sarki Sanusi zuwa ga Buhari

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi Lamido na II ya ce akwai bukatar Shugaba Muhammadu Buhari ya rage albashin ministoci da kuma ‘yan majalisa ke karba a ko wane wata saboda akasarin ‘yan Najeriya na fama da rashin aikin yi.

A cikin wani zancen da Sarki Lamido ya rubutawa Shugaba Buhari ya ce, canjin da gwamnatinsa ke ikirari da shi kamata yayi ya fara daga kan ‘yan majalisar dokokin tarayya.

KU KARANTA:Barayin da suka sace daliban Kaduna sun fadi kudin da za a biyasu kan su saki daliban

“Ina canjin da ake fadi yake? Ta kan majalisar dokokin tarayya ya kamata mu fara ganin canji. Sanata daya yana karbar naira miliyan 36 a ko wane wata guda. Idan aka raba kudin zuwa gida biyu za a iya amfani da sauran miliyan N18 domin samawa ‘yan Najeriya 200 aikin yi da albashin N90,000 a ko wane wata.

“Idan akayi lissafin mutum 200 sau 109 wanda shi ne yawan sanatocin Najeriya za ka samu 21,800 wadanda za a iya sama masu aikin yi. ‘Yan Najeriya da yawa za su iya rayuwa da rabin albashin sanata guda daya kacal.” Inji Sarkin Kano.

A bangare guda kuwa, Sarkin yayi fashin baki a kan kudin da ake biyan ‘yan majalisar wakilai da cewa naira miliyan 25 ne a ko wane wata.

A cikin kalaman Sarkin ya fadi cewa mutanen Najeriya da yawa za su iya amfana idan har gwamnati za ta rage albashin mambobin majalisar dokokin tarayya. Inda ya kara da cewa ko da an raba albashin nasu gida biyu za su yi rayuwarsu cikin walwala kamar yadda suka saba.

https://www.informationng.com/2019/10/senators-receive-n36-million-monthly-yet-nigerians-are-jobless-emir-sanusi.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel