Zaben Bayelsa: Faduwar gaba asarar namiji, Oshiomole yayi martani ga Dickson da PDP

Zaben Bayelsa: Faduwar gaba asarar namiji, Oshiomole yayi martani ga Dickson da PDP

Shugaban jam’iyyar APC a matakin kasa gaba daya, Adams Oshiomole ya ce ko shakka babu dan takarar APC a zaben gwamnan jihar wanda za a yi watan gobe wato Dvid lyon shi ne zai lashe zaben.

Oshiomole ya ce David Lyon ne zai lashe zaben gwamnan ta hanyar lallasa abokin karawarsa na jam’iyyar PDP wato Sanata Diri Duoye.

KU KARANTA:Kunkuru mafi tsufa a nahiyar Afirka ya mutu ya na da shekara 344

Shugaban APC ya fadi wannan maganar ne a jiya Laraba 2 ga watan Oktoba yayin da yake ganawa da tawagar masu ruwa da tsakin APC reshen jihar Bayelsa a Abuja.

Oshiomole wanda yake zargin Gwamnan Bayelsa Dickson da yin amfani da wadansu irin kalamai a lokacin kamfen dinsu, ya ce: “Ba komi ya sa shi fadin wadannan maganganun ba in banda tsoron faduwa zabe.

Ya ce: “Idan ka ji mutum a matsayinsa na gwamna yana ayyana waninsa a matsayin dan-ta’adda saboda bambancin jam’iyyar siyasa to hakika ya fadi kawai.

“Na fahimci inda ya dosa, kasa masu iya magana na cewa ‘fadan da yafi karfinka ai sai ka maida shi wasa’, tsoro ne ya sanya furta wannan magana, saboda ya riga ya hango ya ga faduwarsu na nan biye da su.” Inji Oshiomole.

A wani labarin kuwa zaku ji cewa, EFCC a jihar Zamfara ta cafke wasu ma’aikatan INEC hudu inda ake zarginsu da yin sama da fadi da N84m kudin biyan ma’aikatan da suka yi aikin zabukan gwamna da shugaban kasa da suka wuce.

Ofishin hukumar reshen jihar Sokoto ne ya kama wadannan mutane kuma ya tabbatar mana da cewa da zarar an kammala bincike a kansu za a tura su zuwa kotu.

https://tribuneonlineng.com/bayelsa-2019-pdp-dickson-afraid-of-defeat-%E2%80%95-oshiomhole/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel