Rikicin Gabon da Amina Amal: Kotu ta sanya ranar da za ta yanke hukunci

Rikicin Gabon da Amina Amal: Kotu ta sanya ranar da za ta yanke hukunci

Justis Obiora A. Egwuatu na babbar kotun Kano ya sanya ranar Laraba 23 ga watan Oktoba a matsayin ranar da kotun zata yanke hukunci bisa karar cin-zarafi da Amina Mohammed Amal ta shigar a kan cewa Hadiza Aliyu Gaon ta yi mata.

A ranar Laraban ne kotun za ta dubi wannan karar domin sauraron hujjoji daga bangaren Hadiza Gabon wadda ita ce ake kara. Haka kuma ana sa rana a ranar za a yita ta kare game da karar gaba dayanta.

KU KARANTA:Badakkalar N84m: EFCC ta kama jami’an INEC guda 4 a jihar Zamfara

Amal a cikin karar da ta shigar ta nemi kotu ta ba Gabon umarnin ba ta hakuri a gaban jama’a sannan kuma ta biyata tarar miliyan N50 saboda raunin da ta jimata a fuska.

Sai dai kuma bangaren lauyoyin Gabon sam ba su aminta da wannan abubuwa da Amal ta bukata ba, inda suka cewa ai abin gaba dayansu ya faru ne a can wani wuri na daban inda bai cikin hurumin kotu.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba jim kadan bayan fitowa daga farfajiyar kotun, jagoran lauyoyin Gabon, Barrister Sadiq Sabo Turawa ya ce: “Mun riga da mun mika duk wani bayani da kotun ke bukata na a dakatar da abinda Amal din ta nema.”

A dayen bangaren kuwa, lauyan Amal, Barrister Faruk Umar ya musanta bayanan takwaransa inda ya ce: “Muna jiran ranar cigaba da shari’a ne saboda mun san cewa hujjojinmu masu nagarta ne kwarai da gaske.”

https://www.dailytrust.com.ng/hadiza-gabon-vs-amina-amal-saga-court-fixes-october-23-for-ruling.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel