Kannywood: Abinda ya sa na fice daga masana'antar Kannywood – Adam A. Zango

Kannywood: Abinda ya sa na fice daga masana'antar Kannywood – Adam A. Zango

Fitaccen jarumin fim din hausa kuma mai shirya wasan hausan da aka fi sani da Kannywood, Adam Zango ya bayyana dalilinsa na ficewa daga masana’antar ta Kannywood.

Jarumin ya fadi dalilinsa ne a cikin wani faifan bidiyo mai tsawon minti tara da ya wallafa a shafinsa na instagram inda yake cewa abokan aikinsa na yi masa hassada.

KU KARANTA:Kaico: Mata da miji sun sayar da diyansu 2 a kan N350,000

Ya kuma musanta zargin da ake yi masa na cewa ya kawo mata masu kananan shekaru a cikin sabon fim dinsa mai suna Sabon Sarki. Wani malamin addinin musulunci ne a Kaduna ya yi masa wannan zargin.

Zango ya ce: “Abokan aikina na masana’antar Kannywood ba su tare da ni yanzu. Ba mai sona kuma ma hassada kawai nake samu daga bangarensu. Suna daukana kamar wani sabon shigowa masana’antar kuma basu bani muhimmanci duk don sun ga Allah ya daukaka ni.

“Kusan 90% na ‘yan wasan Kannywood haushina suke ji saboda kawai sun ga Allah ya daga matsayina ya kere nasu. Har ta kai ga ana biyansu wasu kudi domin su ci min mutunci a shafukan sadarwa na zamani.

“Ganin abin ya kai wannan matakin ne naga ba zan iya cigaba da hakuri ba, shi yasa na bar masana’antar Kannywood din gaba daya domin na kafa tawa masana’antar da ni da ‘yan tsirarun mutanen dake tare da ni.” Inji jarumin.

Bayan ficewa daga masana’antar ta Kannywood, jarumin ya kirkiri sabuwar masana’anta tasa ta kashin kansa wadda ya sanya ma suna Kaddywood.

https://www.premiumtimesng.com/entertainment/kannywood/354807-why-i-left-kannywood-adam-zango.html/amp/?p=354807&__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel