Majalisar dattawa na neman Aregbesola da Dingyadi game da Kwalejin ‘Yan sanda

Majalisar dattawa na neman Aregbesola da Dingyadi game da Kwalejin ‘Yan sanda

Majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata 24 ga Satumba ta nemi Ministan lamurran ‘Yan sanda Maigari Dingyadi da kuma na harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola da su bayyana a gabanta.

Kari a kan wadannan mutum biyu, majalisar ta kira Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu a kan sanin musabbabin tabarbarewar tsaro a Najeriya da kuma isalin Kwalejin ‘yan sanda wadda ke karamar hukumar Tai cikin jihar Ribas.

KU KARANTA:UNGA: Najeriya ba za ta ba duniya kunya ba – Buhari

Sanata mai wakiltar Ribas ta Gabas, Mpigi Barinda shi ne ya fara gabatar da wannan kudiri a gaba majalisar wanda kuma daga bisani ya samu goyon bayan wasu mutum tara a majalisar dattawan.

Sanata Mpigi a cikin wata doguwar muhawarar da ya tafka a majalisar, ya bayyana gazawar hukumar ‘yan sanda wurin bai wa kasar Najeriya da take bukata.

Ya kuma ce, bude kwalejojin ‘yan sanda na daya daga cikin hanyoyin sama wa kasa tsaro mai inganci, wanda ya hada da zakulo ma su laifi cikin gaggawa.

Mpigi ya ce: “Kwalejin ‘yan sandan Tai ta na daf da durkushewa saboda halin da take ciki a yanzu abin ka tausaya ne. A maimakon ta kasance wurin horon jami’an ‘yan sanda sai ta zame hoto kawai domin babu kayan aiki a yanzu.

“Akwai bukatar a duba al’amarin wannan kwalejin cikin gaggawa saboda abinda aka bude ta domin shi ba a samun shi daga gareta a yanzu. Ina mai kara fada manufar kwalejin shi ne samawa jihar Ribas da ma Najeriya gaba daya tsaro ta hanyar fito da jaruman ‘yan sanda ma su hazakar aiki.”

https://thenationonlineng.net/senate-summons-aregbesola-dingyadi-over-police-colleges/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel