Damisa ta kashe wani mafarauci a wata kasar Turai

Damisa ta kashe wani mafarauci a wata kasar Turai

Wata damisa ta hallaka wani mafarauci har lahira a gabashin yankin kasar Russia wato Khabarovsk wanda ke kusa da kasar China.

Rahotannin da muka samu a ranar Talata 24 ga watan Satumba sun tabbatar mana da cewa damisar ta kashe mafaraucin ne a daidai lokacin da ya shiga harbarta yayin da take kalace da barewa.

KU KARANTA:Ba zan iya bar wa mijina diyana ba, wata mata ta shaidawa kotu

Haka kuma mafarautan su biyu ne amma mutum guda damisar ta samu kashewa. Sun hadu da kalubale kala-kala tun daga wuirn da suka sauko a kwale-kwalensu.

A lokacin da damisar ta kashe mutum guda, dayan abokin tafiyan nasa ya buda wuta ga damisarsa da bindigarsa, wadda wani mai fafutukar kare hakkin dabobi ya kubutar.

Shugaban kungiyar Kungiyar Amur Tiger centre, wato Sergi Aramilev ne ya sa aka samawa damisar hanyar da har ta iya guduwa.

Mun samu karin bayanin cewa damisoshin Amur Tiger centre a tsare suke a ko da yaushe kuma maganar wannan laifi ana kan gudanar da bincike.

Akwai damisoshi kusan 500 a karkashin wannan kungiya wadanda ake amfani da fatarsu, hakora da kuma wadamsu sassan jikinsu.

Idan zaku iya tunawa, a watan Maris din wannan shekarar wani manomi ya kashe damisar Amur guda daya a lokacin da ya ce ta nemi hallaka shi tare da dabbobinsa.

A wani labarin kuwa, za ku ji cewa, wata mata mai suna Jamila Muhammad ta nemi kotu da ba ta damar rike diyanta guda uku bayan mai gidanta ya saketa.

Jamila dai ta kai karar mijinta ne mai suna Umar Sani a wata kotun shari'ar musulunci dake zaune a unguwar Rigasa a garin Kaduna.

https://www.premiumtimesng.com/foreign/world-foreign/354119-rare-russian-tiger-kills-hunter-who-encroached-on-territory.html/amp/?p=354119&__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel