Daukaka kara: Alkalai 7 da zasu saurari karar Atiku a kotun koli

Daukaka kara: Alkalai 7 da zasu saurari karar Atiku a kotun koli

Tun bayan da jam'iyyar PDP da dan takarar ta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, suka bayyana niyyarsu ta daukaka kara ake hasashe a kan alkalan da zasu saurari karar kuma su yanke hukunci a kanta.

A yanzu haka kotun koli na da alkalai 17 kuma daga cikinsu ne 7 zasu saurari karar da Atiku ya daukaka bayan kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa ta yi watsi da bukatarsa ta neman ta haramta zabenn shugaban kasa, Muhammadu Buhari, tare da bayyana shi a mtsayin zababben shugaban kasa.

Manyan alkalan kotun guda 7 a yanzu haka sune; Jastis Tanko Muhammade (alkalin alakali na kasa), Jastis Bode Rhodes-Vivour, Jastis Mary Odili, Jastis Nwali Ngwuta, Olukayode Ariwoola, Musa Datijo Muhammad da Kumai Bayang Akaahs.

Sai dai, shugaba Buhari ya umarci hukumar kula da bangaren shari'a (NJC) ta kara manyan alkalai shidda a kunshin alkalan kotun koli a karshen shekarar da ta gabata.

Ragowar alkalan kotun sun hada da; Jastis Amina Augie, Jastis Amiru Sanusi, Jastis Adamu Galinge, Jastis Inyang Okoro, Jastis Cletus Nweze da Uwani Abba-Aji da sauransu.

DUBA WANNAN: Kudin yakin neman zabe: Shekarau, Wali da Mansur sun shiga 'tsaka mai wuya'

A ranar Litinin ne Atiku da PDP suka shigar da kara a gaban kotun koli domin kalubalantar hukuncin kotun sauraron korafin zabe da ya tabbatar da sake samun nasarar shugaba Buhari a zaben 2019.

A ranar 11 ga wata ne kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa a karkashin jagorancin Jastis Mohammed Garba ta yi watsi da karar da Atiku da PDP suka shigar.

Kotun ta karanta dukkan korafi 5 da Atiku da PDP suka gabatar a gabanta, kuma ta yi watsi da dukkansu.

Jastis Mohammed ya ce masu kara sun gaza tabbatar wa da kotun cewa suna da hujjojin da zata amince da bukatunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel