‘Yan sanda sun kama wani fitinanne mai kisan mutane a jihar Rivers (Hotuna)

‘Yan sanda sun kama wani fitinanne mai kisan mutane a jihar Rivers (Hotuna)

A ranar Alhamis 19 ga watan Satumba, 2019 ne rundunar ‘yan sandan Najeriya ta samu nasarar damke kasurgumin mai kisan mutanen nan, Gracious David a jihar Rivers.

David mai shekaru 26 ya shiga hannun ‘yan sanda ne a kan hanyarsa ta zuwa Uyo. David daya ne daga cikin ‘yan kungiyar shan jini ta Degbam. Kuma daga lokacin da aka kama shi zuwa yanzu rundunar ‘yan sandan ta ce ya sanar da ita bayanai masu matukar amfani.

KU KARANTA:Abinda ya sa muke neman sulhu da ‘yan bindiga, inji Sufeto janar na ‘yan sanda

‘Yan sanda sun kama wani fitinanne mai kisan mutane a jihar Rivers (Hoto)
Gracious David
Asali: Twitter

Majiyar ‘yan sandan ta sanar da mu cewa an cigaba da bincike akan wannan mutum domin gano ire-iren ayyukan da yake shirin aikata gabanin a kama shi.

‘Yan sanda sun kama wani fitinanne mai kisan mutane a jihar Rivers (Hotuna)
CP Dandaura da David
Asali: Twitter

Mustapha Dandaura, Kwamishinan ‘yan sandan jihar zai zanta da manema labarai a ranar Juma’a 20 ga watan Satumba, 2019 game da kamen wannan mutum.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel