Mayakan Boko Haram sun fara gudu su na barin Najeriya – Rundunar soji

Mayakan Boko Haram sun fara gudu su na barin Najeriya – Rundunar soji

Rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwar cewa a sakamakon ruwan wutan da take yiwa ‘yan Boko Haram, ya sanya mayakan sun fara gudu su na shiga kasashen dake makwabtaka da Najeriya domin neman tsira.

A cikin wani zancen da mai magana da yawun rundunar sojin, Kanal Sagir Musa ya fadi ya ce ayyukan Operation Lafiya Dole da kuma na dakarun tsaron hadin gwiwa ya rikirkita mayakan Boko Haram ta hanyar kashe su da kuma rusa wuraren buyarsu.

KU KARANTA:Sojoji sun kwato mutum 8 daga hannun masu garkuwa a Kaduna

Kanal Sagir ya ce: “Rundunar sojin kasa ta Najeriya na farin cikin sanar da jama’a cewa a bisa nasarorin da dakarunmu ke cigaba da samu wurin yaki da Boko Haram, da dama daga cikinsu na ta yin hijira zuwa wasu kasahen Afirka.

“Labari ya zo mana cewa mayakan na komawa kasashen Chadi da kuma wasu daga cikin kasashen arewacin Afirka. Mayakan na cigaba da watsuwa a kasashen Sudan da kuma Afirka ta tsakiya sakamakon matsin lambar da suke samu a Najeriya.”

A cikin zancen nasa, Kanal Musa ya ambaci kasashen Kamaru, Chadi, Nijar a kan iyakarsu da Najeriya a matsayin wuraren da mayakan suka yada zango.

Kuma ya kara da cewa hukumar tsaron hadin gwiwa tare da rundunarsu ta tuntubi kasashen da abin ya shafa domin sanar da su na su dauki matakin da ya dace.

https://thenationonlineng.net/boko-haram-fleeing-to-neighboring-countries-army-claims/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel