Matasan Najeriya sun tashi tsaye don yaki da luwadi da madigo a kasar

Matasan Najeriya sun tashi tsaye don yaki da luwadi da madigo a kasar

Matasan Najeriya a karkashin hukumar matasan Najeriya ta kasa, National Youth Council of Nigeria sun tashi tsaye domin yaki da miyagun aikin luwadi da madigo a Najeriya ta hanyar gudanar da zanga zangar kyamatar hayalayen biyu.

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito mataimakin shugaban NYCN, reshen yankin Arewa ta tsakiya, Akoshile Mukhtar ne ya jagoranci wannan zanga zanga da suka gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 18 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Kalli yadda Sojojin Najeriya suka gasa wani mutumi da wuta kamar kaza

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Akoshile yana cewa suna yaki da kungiyoyin luwadi, madigo, da ire irensu saboda munanan dabi’u ne a tsakanin al’umma, don haka suke kokarin kawar dasu daga cikin al’umma.

Akoshile ya yi kira ga iyaye dasu kasance masu sanya idanu a kan yayansu, tare da tarbiyyantar dasu bisa kyawawan dabi’u domin su kauce ma afkawa tarkon mutane masu aikata wadannan munana dabi’u.

“Ina kira ga duk wani matashin Najeriya dake sha’awar shiga ire iren kungiyoyin nan daya kauce ma yin hakan saboda wannan ba dabi’ar mutanen Najeriya, kuma baya cikin al’adunmu, haka zalika mutum zai janyo ma kansa fushin Allah, dabbobi ne kadai suke irin wadannan halaye.” Inji shi.

Daga karshe Akoshile ya yi kira ga matasa dasu kai musu karar duk mutumin da suka kama yana aikata luwadi da madigo domin su yi maganinsa tare da daukan matakin fitar dashi daga cikin al’umma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel