Kai mutum ne mai amana, Keyamo ya yabawa Pantami

Kai mutum ne mai amana, Keyamo ya yabawa Pantami

Ministan lamuran Neja-Delta, Festus Keyamo SAN ya yabawa Dr Pantami inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai gaskiya, hazika da kuma rikon amana wanda ya ce yana matukar mutuntawa.

Keyamo ya ce: “Mutane kalilan ne kadai za su iya gayyata ta in halarci taronsu cikin dan takaitaccen lokaci, daya daga cikin wadannan mutane kuwa shi ne ministan sadarwa.

KU KARANTA:Kuyi amfani da fasahar zamani domin kawo karshen matsalar tsaro – Gwamnatin tarayya ta shawarci gwamnoni

“A cikin dan kankanin lokacin da na san shi mun kasance abokai masu ganin girman juna. Gaskiyarsa da rikon amanarsa ke kara sa nake mutunta shi.”

Keyamo ya fadi wannan maganar ne wurin wata liyafa da abokan Dr Isa Ali Pantami suka shirya masa domin taya shi murnar zama minista.

Daga cikin wadanda suka halarci wannan liyafar akwai, Dr Garba Abari Darakta Janar na NOA, Shugaban hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta, Kashifu Inuwa Abdullahi Darakta janar na NITDA da wasu manya-manyan mutane.

A wani labarin mai kama da wannan za kuji cewa, ministan sadarwa Dr Pantami yayi kira ga hukumar NITDA da sauran takwarorinta na su kara tashi tsaye domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ministan yayi wannan maganar ne a lokacin da ya halarci taron mika wa hukumar ta NITDA shahadar ISO 27001: 2013 wanda yake da hurumin aiki tsakanin kasa da kasa.

https://daylightreporters.com/2019/09/19/you-are-trustworthy-keyamo-tells-pantami/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel