Wani Musulmi ya fille kansa saboda tsananin alhinin shiga sabuwar shekarar Musulunci

Wani Musulmi ya fille kansa saboda tsananin alhinin shiga sabuwar shekarar Musulunci

Kasassabar wani mutumi ta ja masa, inda har ma tayi sanadiyyar ajalinsa yayin da yake baki ciki tare da alhinin zuwan watan Al-Muharram na sabuwar shekarar Musulunci na 1441 a kasar India, inji rahoton The Nation.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan mutumi dan Shia mai suna Mohammad Sayum ya kashe kansa ne ta hanyar fille kansa da kansa da wata zaftareriyar wuka daka hannunsa yayin da yake wasa da ita, duk a cikin bakin cikin kisan Hussaini, jikan Annabi Muhammad (SAW).

KU KARANTA: Ba zan sake yin zanga zanga a Najeriya ba – Inji wani babban dan adawan Buhari

Wannan lamari dai ya faru ne lardin Nalanda, na yankin Bihar a gabashin India, inda jama’a Musulman yankin su kanyi bikin sabuwar shekarar Musulunci, sai dai ko da Sayum dan shekara 60 ya aikata ma kansa wannan aika aika, an yi gaggawar garzayawa da shi zuwa Asibitin Sadar, amma ina, aikin gama ya gama.

A duk shekara mabiya Shia suna gudanar da gangami don nuna damuwarsu tare da alhinin mutuwar Imam Hussaini a hannun Sojojin Kalifa Yazid a yakin Karbala wanda ya gudana a shekarar 680 AD.

Daga cikin wannan gangamin alhinin da suke yi, su kan daki jikkunansu, su shiga cikin garwashin wuta, yankan jikkunansu, dukan kirji, marin fuska da dai sauran abubuwan nuna takaici iri iri.

Ko a Najeriya ma mabiya Shia sun gudanar da kwatankwacin wannan alhini, sai dai su basu kai ga yanka jikinsu ko kashe kansu ba, amma dai sun gudanar da zanga zanga a garuruwa daban daban, wanda hakan ya kawo rikici tsakaninsu da Yansanda, har ta kaiga an yi asarar rayuka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel