Kar kuyi gaggawa wurin neman tara dukiya, sakon Magu ga ‘yan Najeriya

Kar kuyi gaggawa wurin neman tara dukiya, sakon Magu ga ‘yan Najeriya

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin-hanci da kuma hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu a ranar Alhamis 12 ga watan Satumba, 2019 ya shawarci al’ummar Najeriya a kan illar neman tarin dukiya cin gaggawa.

Magu ya yi wannan kiran ne a Kaduna yayin da ya halarci wani shirin hira ta musamman da gidan rediyon Nagarta, inda yayi magana a kan ayyukan da hukumarsu ke yi.

KU KARANTA:Assha: Wata mata ta kashe kanta saboda mijinta ya hanata shan sigari

Shugaban hukumar EFCC reshen jihar Kaduna, Mailafia Yakubu ne ya wakilci Magu wurin shirin mai suna ‘Rana mudun aiki’.

Da yake mayar da martani ga tambayoyin masu sauraron shirin da suka samu damar kiran wayar tarho, Magu ya fadi nasarar da hukumarsu ta samu a karkashin ofishin reshen jihar Kaduna.

Bugu da kari, ya sake fadin hanyoyin da al’umma za su iya tuntubar ofishin hukumar domin kai kara ko korafi game da abinda ya shige masu duhu.

A cewarsa, da dama daga cikin matsalolin da hukumar ke haduwa da su a kwanakin nan sun shafi damfara ne ta hanyar amfani da yanar gizo.

Ya kuma kara da yin kira ga iyaye, inda ya roke su da su sanya idanu ga ‘ya’yansu saboda abinda ke faruwa a yau na damfarar yanar gizo matasa ne suke yawa a cikinsa.

Masu sauraron da suka samu damar kiran waya sun yabawa irin ayyukan da hukumar take yi, inda kuma suka roki sauran hukumomi da su yi koyi da hukumar EFCC domin kawo karshen matsalolin cin-hanci da rashawa a Najeriya.

https://www.vanguardngr.com/2019/09/magu-to-nigerians-dont-be-in-haste-to-make-money/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel