Miliyoyin ‘yan Najeriya na cikin matsananciyar wahala ne a dalilin cin-hanci da rashawa – Buhari

Miliyoyin ‘yan Najeriya na cikin matsananciyar wahala ne a dalilin cin-hanci da rashawa – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata 10 ga Satumba ya ce cin-hanci da rashawa ne dalilin da ya sanya miliyoyin ‘yan Najeriya cikin halin bakar wuya.

Haka kuma Shugaban kasan ya kara da cewa cin-hanci da rashawa shi ne babban musabbabin dakilewar cigaban tattalin arzikin Najeriya a bangarori daban-daban na hukumomin kasar nan.

KU KARANTA:Zaben 2019 :Dino Melaye ya daukaka karar hukuncin da kotun zabe ta yanke masa

Shugaban kasan yayi wannan jawabin ne a wurin wani taro na musamman wanda kungiyar ICAN ta shirya a babban birnin tarayya Abuja karo na 49.

Taken taron kuwa shi ne “Gina Najeriya domin samar da cigaba mai dorewa. Ina rokonku da ku dubi cin-hanci da rashawa a rigarsa ta ainihi. Cin-hanci da rashawa shi ne sanadiyar jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali na tsanani.” Inji Shugaban kasan.

Ya kara da cewa, cin-hanci da rashawa yana matukar yiwa ayyukan gwamnati illa a bangaren kawo cigaba da ababen more rayuwa. Ta wannan hanyar ne ake sace kudaden jama’a da ya kamata ayi muhimman aiki da su.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya wakilci shugaban kasan a wurin taron, inda ya ce: “Yakinmu da cin-hanci ba na wasa ba ne da gaske muke yi kuma manufarmu ita ce gina kasa cikin aminci da nagarta.

“Cin-hanci ne yake hana kasar mu cigaba saboda a wuraren da ya kamata a ce anyi aiki sai a ki yi saboda sabo da rashawa. A dalilin cin-hanci ne muka rasa isassun kayan aiki da kuma likitoci a asibitocinmu. Rashawa babu abinda take yi illa kashe kasa, idan har bamu durkushe rashawa ba a kasar nan to hakika rashawa za ta ga bayanmu.” A cewarsa.

https://leadership.ng/2019/09/10/millions-of-nigerians-suffering-because-of-corruption-buhari/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel