An samu rabuwar kai tsakanin wasu yan madigo yayin da ‘Mata’ ta harbe ‘Mijinta’

An samu rabuwar kai tsakanin wasu yan madigo yayin da ‘Mata’ ta harbe ‘Mijinta’

Wasu mata biyu da suka yi auren jinsi, watau yan madigo sun shiga bakin jama’a bayan guda daga cikinsu wanda ita ce ‘matar’ ta dirka ma dayar wanda ita ce ‘mijin’ alburusai har sau 11 da nufin kasheta saboda ta kamata tana cin amanarta.

Rahoton jaridar Gistreel ta bayyana cewa wannan lamari ya auku ne a jahar Detroit na kasar Amurka, inda Airrion Wallace ta bayyana cewa abokiyar zamanta wanda suka kwashe tsawon shekaru 12 tare, ta harbeta saboda ta tuhumeta a kan cin amana.

KU KARANTA: An kashe mutum 1 a sanadiyyar rikici tsakanin manoma da makiyaya a Jigawa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Wallace tana cewa: “Na fada ma matata abin da ta yi bai dace ba, har ma na yi barazanar shigo da wata matar nan gidan don ta ji idan cin amana da dadi, don haka na nemi kawai mu raba auren namu saboda b azan jure cin amana ba.

“Daga nan sai na ji tace “Da ni zaka yi wasa?” kawai zai ta zaro bindiga, ta dinga harbina har sau 11, ta harbeni sau 4 a gabana, sau 4 a kafana, sai kuma sai 3 a cikina, amma na daddage na fita daga gidan don tsira da raina, Allah Yasa akwai jama’a a kofar gida, wanda suka kira mata Yansanda.

“Sai dai ta shaida ma Yansanda cewa wai ta yi haka ne don kare kanta, tunaninta shine idan na rabu da ita babu wanda zai iya zama da ita.” Inji Wallace.

Tir, Allah wadaran naka ya lalace, duka wadannan mata fa da ake magana bakaken fata ne, wadanda turawa suka nuna musu yancin auren jinsi, Allah Ya karemu daga sharrin mugun ji da mugun gani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel