Da dumi dumi: Kamfanin MTN ta kulle ofisoshinta gaba daya dake Najeriya

Da dumi dumi: Kamfanin MTN ta kulle ofisoshinta gaba daya dake Najeriya

Hukumar kamfanin MTN ta sanar da garkame dukkanin kamfanoninta da ofisoshinta har sai ‘Baba ta ji’ sakamakon hare haren ramuwar gayya da wasu yan Najeriya suka fara kai mata biyo bayan cin zarafi tare da kashe yan Najeriya da ake yi a kasar Afirka ta kudu.

Jaridar Pulse ta bayyana cewa MTN, wanda kamfanin kasar Afirka ta kudu ne ta sanar da rufe ofisoshin nata ne a ranar Laraba, 4 ga watan Satumba sakamakon an fara farfasa kai mata hari wasu jahohin Najeriya, inda har ma an kona mata ofisoshi.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Ana harbe-harbe a kantin Shoprite da ke Owerri

Wannan shine karo na farko da yan Najeriya ke ramuwar gayyar abinda yan kasar Afirka ta kudu su ke yi ma baki a kasarsu, inda a wannan karo sun kashe baki yan Afirka, da dama daga cikinsu yan Najeriya, tare da kona shagunan yan Najeriya fiye da 50.

A cewar MTN: “A kwana daya daya gabata, an kakkai ma ofisoshinmu hari, da ma abokan huldarmu a matsayin harin ramuwar gayyar abin dake faruwa a kasar Afirka ta kudu na harin kyamatar baki yan Afirka, muna da tabbacin harin da aka kai ma ofisoshinmu dake Legas, Ibadan da Uyo.

“Muna da niyyar cigaba da aikinmu na gamsar da abokan huldarmu, amma bamu da tabbacin tsaron ma’aikatanmu, da abokan huldarmu, don hakamun kulle duk wasu ofisohinmu har sai ‘Baba ta ji’.” Inji sanarwar.

A wani labarin kuma, Najeriya ta yi ma jakadanta dake kasar Afirka ta kudu, Kabiru Bala, kiranye domin nuna bacin ranta game da abubuwan dake faruwa a kasar Afirka ta kudu na kai ma baki yan Afirka hari, musamman yan Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel