Wadume ya yi kuskure da ya nemi mafaka a jihar Kano - Ganduje

Wadume ya yi kuskure da ya nemi mafaka a jihar Kano - Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umaru Ganduje, ya bayyana cewa madugun mai garkuwa da mutane na jihar Taraba da aka sake kamawa, Hamisu Bala wanda aka fi sani da Wadume ya yi kuskuren neman mafaka a jihar Kano.

Gwamnan, yayin da yake magana da yan jarida jiya Lahadi, 1 ga watan Satumba a Yola, ya bayyana cewa tarin tsaron da aka zuba ba zai bar yan fashi suyi aiki ba a jihar.

Ya bayyana cewa babu dan fashin da zai shiga jihar Kano ya share mako daya ba tare da jami’an tsaro sun cafke shi ba saboda yanayin tsaro da aka kafa a cikinta.

Ganduje ya kara da cewa a Kano aka kama gawurtaccen dan ta'addan da yayi garkuwa da Sarkin Magajin Daura daga jihar Katsina kuma har ila yau, anan aka kama shugaban yan fashin da ya kai hari kan tawagar mataimakin gwamnan jihar Nasarawa inda mutane hudu suka rasa ransu.

Ban da wannan, gwamnan jihar Kano ya bayyana cewa karfafa cibiyoyin ilimi da kuma mayar da ilimi abu mai muhimmanci ga gwamnati da kuma inganta matasa ya taimaka ma gwamnatinsa a fannin kau da laifuffuka a jihar.

KU KARANA KUMA: Gamayyar kungiyoyin Arewa ta sha alwashin daukar mataki kan raina 'yan yankin

Daga karshe, gwamnan ya bayyaa cewa jami'an tsaro masu sanya inifam kadai ba za su iya agance matsalolin tsaro ba a kasar, har ai al'umman kasarsun basu dajin kai domin taimaka masu da bayanai na kwararru da sauran muhimman bayanai.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel