Hanyar Kaduna-Abuja: Abokina ya rabu da zuwa gonar kajinsa saboda masu garkuwa da mutane, inji Shehu Sani

Hanyar Kaduna-Abuja: Abokina ya rabu da zuwa gonar kajinsa saboda masu garkuwa da mutane, inji Shehu Sani

-Shehu Sani ya koka a kan halin da hanyar Kaduna-Abuja ke ciki a yau na sace-sace da garkuwa da mutane

-Tsohon sanatan ya ce abokinsa Alhaji Hamza ya rabu za zuwa gonar kajinsa dake hanyar saboda wannan al'amarin dake faruwa bisa hanyar

Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya koka a kan yadda hanyar Kaduna-Abuja ta zama sansanin masu garkuwa da mutane inda ba a jimawa sai kaji anyi gaba da bil’adama a kan hanyar.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita @ShehuSani a ranar Asabar 31 ga watan Agusta, ya ce abokinsa Alhaji Hamza ya rabu da leka gonarsa da ke hanyar Kaduna-Abuja.

KU KARANTA:Lantarki: Gwamnatin tarayya ta kammala aikin da zai samar da karin 40MW na wutar lantarkin

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mana cewa Sani na fadi cewa abokin nasa ya kasance yana zuwa gonar ta sa ne da can a kowace ranar Asabar amma tuni yayi watsi da zuwa gonar.

A cewar Shehu Sani: “Lokacin da mutanen kauyen da gonar tasa take suka kira shi domin sanar da shi halin da kajinsa ke ci, sai ya ce da su ku gaishe su kawai.”

A wani labarin mai kama da wannan, Shehu Sani ya ce ‘yan siyasan Najeriya na nan na yin shiri domin magance farmaki da ake kai masu a kasashen waje.

Sani yayi wannan maganar ne biyo bayan harin da ‘yan kungiyar IPOB suka kaiwa Ike Ekweremadu tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya a kasar Jamus.

Shehu Sani ya ce: “Akwai wata kungiya da ta gayyace ni domin gudanar masu da wani jawabi na musamman a birnin Landan, sai na ce dasu su nemi allo su rubuta tsohon sanata su bani domin yanzu na ga abinda ake yayi kenan na farma ‘yan siyasa a kasar waje.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel