Kannywood: Abinda yasa aka rabu da gani na a cikin fina-finai – Nuhu Abdullahi
Fitaccen dan wasan hausan nan wanda ake yiwa lakani da Kannywood, Nuhu Abdullahi wanda yake fitowa a cikin fim tare da shirya na shin a kansa. An wata hira da jarumin inda yake fadin dalilin rashin ganinsa cikin fina-finai a ‘yan kwanakin nan da kuma rikice-rikice da ke faruwa a masana’antar ta Kannywood.
Mujallar karshen mako: Mun jima bamu ganinka cikin sabbin fina-finai, shin ka bar masana’antar ne?
Nuhu Abdullahi: A’a ba haka bane, ina nan a masana’anta har ila yau. Dalilin dauke kafata kuwa ya kasance ne saboda siyasa da na shiga domin goyon bayan wasu ‘yan takaran da muke da yakinin cewa zasu kawo mana cigaba.
KU KARANTA:Hadiza Gabon ta tallafawa Maryam KK da makudan kudade akan iftila'in da ta fada na shiga hannun 'yan bindiga
Nine jigorawan kamfen din Buhari-Osinbajo 2019 a masana’antar Kannywood. A cikin tawagata kuwa duk ‘yan wasan hausa ne maza da mata, kun ji abinda ya dauki lokacina kenan ‘yan kwanakin nan.
Mujalla: Ya kake kallon al’amarin rashin fahimta tsakanin ‘yan wasa da kuma hukumar tantance fina-finai ta Kano?
Nuhu Abdullahi: Abinda ke faruwa bana jin dadinsa gaskiya, a dalilin abinda ke faruwa ‘yan kasuwa da dama sun fita daga masana’antar fim zuwa wani abu na daban. Bamu bukatar sai mun fadawa wani cewa masana’antar Kannywood na durkushe a halin yanzu saboda irin wannan rashin jituwar.
Mujalla: Baka tunani buga fina-finai na jabu ne kashe masana’antar ba hukumar tace fina-finai ba?
Nuhu: Yauwa yanzu da ku kawo maganar buga fina-finai cikin faifai na jabu kun fadi hakikanin inda matsalar take. Amma ina so kusan abu daya dakile sayar da jabun faifan fina-finai aikin hukumar tacewa ne amma bata yin aikinta yadda ya dace.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng