Kisan babban malamin addini: IGP ya yi umurnin tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin bauta

Kisan babban malamin addini: IGP ya yi umurnin tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin bauta

Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, a daren jiya Alhamis, 29 ga watan Agusta, ya nuna matukar damuwa akan hare-haren baya-bayan nan da ake kaddamarwa akan malaman addini a wasu yankunan kasar.

Ya umurci kwamishinonin yan sanda a dukkanin jihohin tarayya da babbar birnin tarayya kan cewa daga yanzu su mayar da hankali sosai akan malamai sannan su kara tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin bauta a fadin kasar.

Kakakin rundunar, DCP Frank Mba, a wani jawabi da ya saki, Shugaban yan sandan ya umurci kwamishinan yan sanda a jihar Taraba da ya tsamo makasan Rev. Father David Tanko wanda, a cewarsa, wasu da ba a san ko su wanene ba suka kashe shi a farkon ranar 29 ga watan Agusta, a kauyen Kpankufu da ke hanyar Wukari a hanyarsa ta zuwa kauyen Kofai Ahmadu a jihar Taraba.

Mba yace IGP yayi ta’aziyya ga ahlin katolika a Najeriya an lamarin.

KU KARANTA KUMA: Kisan jami’an tsaro: Rahoton kwamitin bincike na kawo jinkiri wajen shari’ar sojoji

Yace Shugaban yan sandan ya kuma umurci DIG da ke kula da sashin bincike na rundunar da za samar da karin kayayyakin bincike a rundunar na jihar Taraba domin taimakawa wajen binciken lamarin.

Mba ya kuma bayyana cewa IGP ya umurci mutane da su kwantar da hankalinsu tare dab a yan sanda cikakken goyon baya a kokarinsu na gano masu laifi, kudirinsu da kuma dalilinsu na kashe malamin addinin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel