Uwargidar gwamnan Kogi ta ginawa wata tsohuwa gida sannan ta kawata shi da kayan alatu (hotuna)

Uwargidar gwamnan Kogi ta ginawa wata tsohuwa gida sannan ta kawata shi da kayan alatu (hotuna)

Uwargidar gwamnan jihar Kogi, Misis Rashida Yahaya Bello, ta tallafa wa wata tsohuwa mai suna, Misis Salihu Uhuanamo a yankin Ipaku-Eba da ke aramar hukumar Adavi na jihar da muhallin zama.

Tsohuwar na cikin tsananin bukata na wajen zama hakan ya sanya Misis Bello gina mata gida mai dauke da dakuna biyu tare da kawata mata shi da kayan more rayuwa.

Matar gwamnan ce ta wallafa hakan a shafinta na Facebook inda tayi godiya ga Allah akan ikon da ya bata na kawo sauyi a rayuwar matar.

Ta kuma bukaci al’umman Kogi da su kasance masu taimakawa mabukata da nuna soyayya da kulawa ga makwabtansu.

Ga yadda tawallafa a shafin nata:

KU KARANTA KUMA: Garin kwaki suka dunga dirka mana har tsawon kwana 8 – Mutanen da aka yi garkuwa da su

A wani labarin kuma, mun ji cewa Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, kuma wacce tauraruwarta ke haskawa a wannan lokaci, Hadiza Gabon ta taimakawa tsohon nan da hotunanshi suka karade shafukan sada zumunta.

Jarumar wacce tayi kaurin suna wajen bayar da taimako ga mabukata da masu karamin karfi a jihohin arewa ta taimakawa tsohon ta hanyar sanyawa a gina masa sabon gida.

Dattijon bawan Allah mai suna Abba Babuga dake karamar hukumar Patiskum a jihar Yobe, ruwan sama yayi awon gaba da gidanshi a wani mamakon ruwa da aka tafka a kwanakin da suka gabata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng