Wata mata za ta shekara 24 a gidan yari saboda ta ki sanya hijabi
-Wata kotun kasar Iran ta yankewa Afshari hukuncin shekaru 24 a gidan yari saboda ta ki sanya hijabi
-Jaridar Daily Mail ta ruwaito cewa Afshari da mahaifiyarta sun dade suna taka dokar da aka sa ta sanya hijab a kasar Iran
Wata mata ‘yar asalin kasar Iran wadda ke fafutukar kare hakkin mata za ta shekara 24 a gidan yari a cikin hukuncin hadda shekaru 15 a gidan yarin na yada fasikanci ta hanyar cire hijabi.
Saba Kord Afshari wadda ke da shekaru 20 a duniya ta samu wannan hukuncin ne ranar Talata daga wata Kotun Tehran bayan da aka sameta da aikata laifin cire hijabinta.tare da yin fito na fito da dokokin kasar.
KU KARANTA:Madalla: Daliban Najeriya sun ciyo lambar yabo ta zinari a kasar Amurka
Jaridar Daily Mail ta ruwaito cewa Afshari da mahaifiyarta Raheleh Ahmadi na kan gaba a cikin wata kungiya mai yakar wajabcin sanya hijabi.
Bugu da kari, wannan matashiya tare da mahaifiyarta sun sha wallafa bidiyo a shafukan sada zumunta ba tare da hijabi a jikinsu ba, domin sanya ra’ayi ga sauran ‘yan kasar ta Iran na su fito babu hijabin.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Iran Human Rights Monitor ta ce an fara kama Afshari ne tun watan Agustan bara a babban birnin kasar Iran.
A ranar 19 ga watan Agusta aka shigar da karar ta kotu inda kuma a ranar 27 ga watan Agusta aka sanar da ita sabon hukuncin da aka yanke mata.
Iran Human Rights Monitor ta ce, an kara tsaurin hukuncin na ta ne saboda bayyana laifukan da ta dade tana aikatawa.
Akwai wasu mata uku da aka yankewa irin wannan hukuncin a ranar Litin a Tehran inda za su shekara 18 a gidan yari. Shima Babaii, Mojgan Lali da Shaghayegh Mahaki ne sunayen matan guda uku.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng