Najeriya ta tura matasa 60 kasar China don koyon yadda ake hada na’urar raba wutar lantarki

Najeriya ta tura matasa 60 kasar China don koyon yadda ake hada na’urar raba wutar lantarki

Hukumar kimiyya da fasaha ta Najeriya, NASENI, ta bayyana cewa kimanin matasa yan Najeriya 60 ne suka wuce zuwa kasar China a ranar Talata, 27 ga watan Agusta domin halartar horo a kan yadda ake hada na’urar rarraba wutar lantarki, Turansifoma.

Kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito mataimakin daraktan watsa labaru na NASENI, Olusegun Ayeoyinikan ya bayyana haka, inda yace manufar hukumar shi ne kafa wata cibiya a Najeriya da za ta dinga kera Turansifoma a karkashin jagorancin yan Najeriya, tare da amfani da kayan gida.

KU KARANTA: Yan Najeriya na kashe naira biliyan 400 wajen biyan cin hanci da rashawa a shekara – ICPC

Mista Olusegun yace za’a kafa wannan cibiya ne a cikin cibiyar sarrafa na’urorin wutar lantarki, PEEMADI dake karkashin ikon NASENI dake garin Okene na jahar Kogi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar NASENI, Farfesa Mohammed Haruna ne ya yi jawabin ban kwana ga injiniyoyin da suka tafi China, inda ya bayyana farin cikinsa da wannan dama da suka samu na halartar horon da za’a kwashe tsawon watanni 4.

Shugaban ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministan kimiyya da fasaha na Najeriya, Ogbonnaya Onu bisa amincewar da suka nuna masa na gudanar da aikinsa yadda ya kamata, haka nan ya jinjina ma kamfanin Chinese Great Wall Industry Corporation, CGWIC da suka hada gwiwa da gwamnati a kan wannan aiki.

Farfesa Haruna yace da zarar injiniyoyin sun dawo Najeriya, za’a basu daman aiwatar da ilimin da suka samu wajen harhada kayan aikin da ake bukata a fannin wutar lantarki, daga ciki har da Turansifoma.

Daga karshe Farfesan ya koka kan yadda ake shigo da Turansifomomi Najeriya, wanda yace hakan ya hana yan Najeriya samun ilimin kimiyyar hada na’urar, kuma hakan ba zai bari a yi amfani da kayan gida wajen hada na’urar ba.

Tun a shekarar 2013 gwamnatin Najeriya ta shiga yarjejeniya tsakaninta da CGWIC ta hannun NASENI don horas da injniyoyin Najeriya kimiyyar hada na’urar Turansifoma, amma aka gagara aiwatar da yarjejeniyar har sai zuwa shugaban kasa Buhari da minista Ogbonnaya Onu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel