Kowa ya ci zomo ya ci gudu: An bayyana dan Najeriya a matsayin wanda ya fi kowa gudu a Afirka
Wai, ni da zomo, wani dan wasan motsa jiki na Najeriya, Raymond Ekevwo ya lashe kambun mutumin da yafi kowa gudu a yankin nahiyar Afirka gaba daya, a gasar wasannin kasashen Afirka na 2019 dake gudana a kasar Morocco.
Legit.ng ta ruwaito Raymond ya lashe wannan kambu ne bayan ya yi gudun famfalaki na mita 100 a cikin dakika 9.96, yayin da wani dan Najeriya, Usheoritse Itsekiri ya zo na uku daya kammala gudun cikin dakikai 10.02.
KU KARANTA: Barayin mutane sun kashe mutane 3, sun yi garkuwa da wasu a hanyar Kaduna zuwa Abuja
Wannan shine karo na farko tun shekarar 2007 da Najeriya ta samu kyautar zinari a gudun famfalakin mita 100 a gasar motsa jiki na nahiyar Afirka, sai dai kowa a gudun mita 100 na zagayen farko da na biyu, Raymond ne ke lashewa, inda ya kammala a dakika 10.20 da dakika 10.26.
A gudun yada kanin wani na mata kuwa, an yi waje da fitacciyar yar gudun Najeriya, Blessing Okagbare biyo bayan riga malam masallaci da ta yi ma alkalin gudun wajen zurawa a guje tun bai bada umarni ba, don haka yar Najeriyan da ta rage a wasan karshe it ace Joy Udo-Gabriel, kuma a ta hudu ta kare.
Da yake jawabi, Raymond sarkin gudu, ya bayyana farin cikinsa da nasarar daya samu, kuma ya mika godiyarsa zuwa ga Allah daya bashi nasara. “Ina alfahari kasancewata dan Najeriya, tun yanzu na fara shiga fafatawa a gasar tsere na duniya da za’a yi a Doha, Qatar.” Inji shi.
Wadanda suka taba ciyo ma Najeriya lambar zinari a gasar tsere sun hada da Olusoji Fasuba, Chidi Imoh, Davidson Ezinwa da kuma Deji Aliu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng