Wata mata ta haifi diya 5 lokaci guda a wata kasar Afirka

Wata mata ta haifi diya 5 lokaci guda a wata kasar Afirka

-Wata mata a kasar Uganda ta haifi 'ya'ya biyar ba zato ba tsammani

-Matar dai tana tsammanin haihuwar tagwaye ne bayan a dauki hoton cikin nata a wata cibiyar kula da lafiya

-Jaridar Monitor ta ruwaito cewa matar da diyanta na cikin koshin lafiya amma tana bukatar taimakon domin daukar nauyin yaran

Wata mata a kasar Uganda ta haifi jarirai biyar inda uku daga ciki mata ne yayin da ragowar biyun suka kasance maza.

Wata mata ta haifi diya 5 lokaci guda a wata kasar Afirka
Wata mata ta haifi diya 5 lokaci guda a wata kasar Afirka
Asali: Getty Images

Gabanin haihuwar likitoci sun shaida mata cewa tagwaye za ta haifa kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito.

KU KARANTA:Wata sabuwa: Mujallar fim ta kalubalanci Rahama Sadau da amfani da mazaunan roba a wani hoto da ta dauka

Matar mai suna Sofiat Mutesi ta taba haihuwar tagwaye da ‘yan uku kamar yadda jaridar ta bamu labari.

“Nayi matukar mamakin haihuwar ‘ya’ya biyar saboda a lokacin da na je aka dauki hoton cikin nawa a cibiyar lafiya ta Nsinze, likitoci cewa suka yi ina dauke ne da tagwaye,” a matar.

Haka zalika, an ruwaito cewa matar na neman taimako domin daukar nauyin ‘ya’yan nata. Kamar yadda jaridar Monitor ta ruwaito, mijinta na fari ya rasu haka kuma mijinta na yanzu ya na da ‘ya’ya 20.

Maureen Babine, wadda take ungozoma a asibitin da matar ta haihuwa ta ce mahaifiyar da ‘ya’yan nata na cikin koshin lafiya.

“A duk shekarun da nayi ina aiki a asbitin nan ban taba ganin matar da ta haifi diya biyar lokaci guda ba. Muna dai samun ‘yan biyu da ‘yan uku, jariran nata duk sun isa haihuwa sai dai suna bukatar kulawa ta musamman,” a cewar malamar jinyar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel