Dole mijina ya kasance da budurwa – Inji wata Jaruma

Dole mijina ya kasance da budurwa – Inji wata Jaruma

Wata jarumar masana’antar shirya fina-finan Kudu wato Nollywood, Kudirat Ogunro, ta bayyana cewa za ta bari mijinta ya kasance da wata budurwa bayan aurensu domin su samu gida mai cike da zaman lafiya.

Ogunro ta fada ma manema labarai a wata hira a Abuja cewa halin maza ne tara mata.

Ta shawarci mata da su daina yaudarar kansu ta hanyar kokarin mallakar mazajensu su kadai.

“Ni bana soyayya da kishi. Kuma ji, idan nayi aure, ya zama dole mijina ya kasance da budurwa.

“Ta haka ne za a samu zaman lafiya a gidana maimaon ace yana fada mun cewa ni kadai ce masoyiyarsa. Ko kadan, ban yarda da irin wadannan zantukan ba. Da gaske nake.

“Halin maza ne tara mata; don haka mu daina yaudarar kanmu,” inji jarumar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sojoji sun kama motocin yaki guda 6 a Adamawa

A wani labari na daban, mun ji cewa kungiyar masu ladabtar da masu yiwa mata fyade ta jihar Legas ta bukaci a hukunta wani malamin lissafi mai suna Emmanuel Davies, akan zargin shi da ake da kokarin lalata wata dalibarsa karama.

Shugaban kungiyar mai suna Titilola Vivour-Adeniyi, ya ce Davies ana zargin shi da tilasta dalibarsa mai suna Almalohi Ehi Omiunu mai shekaru goma sha hudu (14) da ta dinga tura masa hotunan ta tsirara.

A wata sanarwa da aka fitar ranar 19 ga watan Agustan nan, wacce kuma aka mikawa kwamishinan 'yan sandan jihar Zubairu Mu'azu, shugaban kungiyar ya ce mahaifiyar yarinyar, ta kai musu korafi akan wannan mutumi ranar 5 ga watan Agusta, bayan yarinyar ta kai karar shi ga mahaifiyarta akan abinda yake mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel