Dakarun sojin NAF sun tarwatsa wani gungun mayakan a Bula Korege

Dakarun sojin NAF sun tarwatsa wani gungun mayakan a Bula Korege

-Dakarun sojin NAF sun tarwatsa wata mabuyar 'yan Boko Haram dake Bula Korege a Borno

-Kakakin rundunar sojin NAF Ibikunle Daramola ne ya bada wannan labari inda ya ce abin ya auku ne a ranar Juma'a

Rundunar sojin sama ta NAF ta fitar da labarin cewa mayakan Operation Lafiya Dole na rundunar sun ragargaza wata mabuyar mayakan Boko Haram dake Bula Korege dake kan gabar jejin Sambisa a Jihar Borno.

Kakakin rundunar sojin NAF, Ibikunle Daramola ne ya fitar da wannan labarin inda ya ce a ranar Juma’a ne dakarun suka kai wannan farmaki.

KU KARANTA:Mafi karancin albashi: Maganar ta dawo bisa teburin Buhari

Haka zalika, a cikin zancen nasa ya fadi cewa, dakarun na daga cikin wani shirin na musamman mai suna Operation Green Sweep III wanda ke farautar ‘yan ta’addan dake yankin Borno.

Zance ya kara da cewa, an jima ana kaiwa da komowa kafin dakarun su kai wannan harin domin tabbatar da gaskiyar lamari game da rahotannin sirrin da suka samu game da mabuyar.

Rahotannin wadanda suke na sirri sun tabbatar da cewa wurin ya kasance mabuyar mayakan na Boko Haram da dadewa, kamar yadda rundunar NAF din ta fadi.

“Jiragen yaki wadanda aka fi sa ni da Alpha Jets biyu ne suka kai harin. Wadannan jiragen da dama an tanadesu ne saboda irin wannan aiki. Kuma sun samu nasara a harin da suka kai.

“Harin jiragen ya ragargaza mabuyar ta Boko Haram inda daruruwan ‘yan kungiyar suka mace nan take.” A cewar kakakin NAF.

A karshe kakakin yayi karin bayanin cewa, rundunar sojin NAF za ta samu nasarar kore dukkanin ‘yan ta’addan dake yankin Arewa maso gabas idan har suna samun goyon bayan jami’an tsaron dake aikinsu a kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel