Jerin sunayen Yan Najeriya 80 da aka kama da zambar miliyoyin daloli a kasar Amurka
Rahotanni sun kawo cewa hukumar FBI ta kasar Amurka ta fallasa jerin sunayen wasu mutanen kasar Najeriya 77 da aka samu da laifin yin zambar miliyoyin daloli a kasar.
An tattaro cewa zuwa yanzu wadannan mutane sun bayyana a gaban kotun Amurka inda ake tuhumar su kan aikata laifuka har 252 da ya saba wa dokar kasar.
Hukumar ta ce an gabatar da tuhume-tuhumen ne bayan jami'an tsaro a safiyar ranar Alhamis, 23 ga watan Agusta sun kama mutane 14 a fadin Amurka, 11 daga cikinsu a birnin Los Angeles.
Biyu daga cikin wadanda ake zargin dama suna a hannun hukumomi bisa wasu zarge-zargen na daban,inda kuma aka kama daya daga cikinsu a farkon makon nan.
Sauran wadanda ake zargin na zama ne a kasashen ketare, kuma yawancinsu na zaune ne a Najeriya.
Babban alkalin California Nick Hanna ya ce wannan shari'a wani yunkuri ne na kare yan Amurka daga fadawa hannun masu damfara ta shafukan yanar gizo, da kuma tabbatar da cewa wadanda aka kama da irin wannan laifi sun fuskanci hukunci.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotun zabe ta soke nasararar Dino Melaye a matsayin sanatan Kogi ta yamma
Ga jerin sunayen sun an a kasa:

Asali: UGC

Asali: UGC

Asali: UGC

Asali: UGC

Asali: UGC

Asali: UGC
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng