Ba mu rufe iyakar Kotono ba – Hukumar Kwastam

Ba mu rufe iyakar Kotono ba – Hukumar Kwastam

Rahotanni da ke zwa mana sun nuna cewa Hukumar hana fasa kwauri na Najeriya ta ce ba ta rufe rufe babbar iyakar ta da kasar Benin da ke Seme a jihar Legas ba.

Kakakin hukumar ta Kwastam, Joseph Attah ya ce mutane suna da damar shige da dfice a kasar matukar suna da hujjar yin hakan.

Ya kara da cewa sanarwar da aka fitar ga manema labarai kwanakin baya ta ce wani aikin sintiri ne da ake yi a kan iyakar yake haddasa cunkoso, amma babu wani lokaci da aka taba rufe iyakar.

Sai dai tun da farko wasu 'yan kasuwar da ke hada-hada a iyakar sun nuna rashin jin dadinsu akan al'amarin.

Shafin BBC Hausa ta ruwaito cewa ma'ajin dillalan kungiyar fito da kayayyaki a kan iyakar, Alhaji Zubairu Mai Mala ya ce a yanzu harkokinsu na yan kasuwa sun tsaya cak.

Mista Attah ya ce aikin sintirin wanda aka yi wa inkiya da Ex-Swift Response zai kare kasar daga ayyukan ta'addanci da fashi da makami da fasa kwaurin kayayyaki da shigowa da kananan makamai kasar.

KU KARANTA KKUMA: Zaman lafiya ya samu bayan harin Boko Haram a Borno

Aikin sintirin na hadin gwiwa ne da hukumar da ke kula da shige da fice da 'yan sanda da hukumar kwastam da sauran jami'an tsaron Najeriya, a cewar sanarwar.

Har ila yau, Mista Attah ya ce za a kwashe tsawon kwanaki ana aikin sintirin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel