Toh fah: Al’umma Ibi sun dau zafi akan kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane Wadume, sun ce za su yi kewar kyautatawarsa

Toh fah: Al’umma Ibi sun dau zafi akan kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane Wadume, sun ce za su yi kewar kyautatawarsa

Kama Hamisu Wadume ya jefa al’umman Ibbi, garin gawurtaccen mai garkuwa da mutane mai arziki a jihar Taraba cikin wani irin hali.

Tawagar kwararru na shugaban yan sanda sun sake kama mai garkuwa da mutanen wanda wasu sojoji suka kubutar a baya bayan sun kashe yan sanda uku da dan farin hula daya, a ranar Litinin, 19 ga watan Agusta, a unguwar Lai Mai da ke yankin Alo Holo a jihar Kano.

Sai dai kuma wasu mazauna yankin Ibi sun dauki zafi akan kamun nasa yayinda suka bayyana cewa za su yi matukar kewar kyautatawarsa, ciki harda gina wani masallaci da yayi ga mutanen garinsa.

“Labarin kama shi ya zo ma mutanen Angwan Motori a Serkin Kudu da ke Ibbi a jihar Taraba a matsayin abun bakin ciki; da sauran mutane wadanda suka amfana daga kyautatawarsa.

“Ya kasance mutum mai kyautatawa kuma baya nuna bambamci ga kabilu ko addini."

Yahaya Maikifi Ibi ya fada ma jaridar Punch cewa “Wadume a halin yanzu yana kan gudanar da aikin gina masallaci a yankinmu. An kusa kammala aikin, amman kama shi da aka yi zai janyo koma baya ga aikin.”

KU KARANTA KUMA: EFCC ta zargi magoya bayan Ambode da yi wa jami’anta 3 rauni, da kuma lalata masu abun hawa

Wani dan kauyen yayi nunin cewa Wadume ya gina famfunan ruwa kuma har ila yau yayi kokari wajen kawar da talauci daga wasu gidaje.

Tsohon shugaan rikon kwarya na karamar hukumar Ibi, Adasho Johnson ya kuma yaba da kama Wadume. A cewarsa, kama Wadume shine mafi alkhairi ga kowa da ke zaune cikin halin tsoro akan kamun da jami'an tsaro suka yi bayan tserewar mai garkuwa da mutanen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel