Kungiyar IPOB ta fadi dalilinta na cin mutuncin Ekweremadu a kasar Jamus
Kungiyar masu fafutukar neman kafa kasar Biafra (IPOB) ta bayyana cewa mambobinta sun ci mutuncin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ike Ekweremadu, ne saboda yana daga cikin wadanda suka daure wa gwamnati gindi wajen kaddamar da atisayen 'rawar gansheka (Python Dance)'.
Wasu fusatattun mambobin kungiyar IPOB sun kai wa Ekweremadu farmaki yayin da ya halarci wani taron al'ada na shekara- shekara da 'yan kabilar Igbo ke gudanar wa a Nurnberg da ke kasar Jamus. An gayyace shi ne a matsayin babban bako mai gabatar da jawabi.
A wani faifan bidiyo da ya mamaye kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta a yammacin ranar Asabar, An ga Ekweremadu na barin wurin taron cikin hanzari a wata mota yayin da wasu fusatattun jama'a ke jifansa.
A wani sako da ta fitar a shafinta na Tuwita, Radiyo Bifara, wacce shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, ke jagoranta, ta bayyana cewa an tuhumi Ekweremadu da "hada baki da gwamnatin Najeriya wajen kisan mambobin kungiyar IPOB"
A wani jawabi da IPOB ta fitar ranar Lahadi ta bakin kakakinta, Emma Powerful, kungiyar ta ce ta kai wa Ekweremadu farmaki ne domin yin biyayya ga umarnin shugabansu a kan su hukunta duk wani mai hannu a cikin kulla atisayen 'Python Dance' a yankin kudu maso gabas.
DUBA WANNAN: Jerin sunayen 'ya'yan Buhari da makarantun da suka halarta
Kungiyar ta kara da cewa tun farko saida suka gargadi masu shirya taron a kan kar su gayyato maci amana wurin, amma basu ji ba saida suka gayyace shi.
Powerful ya cigaba da cewa "yanzu haka Fulani makiyaya sun mamaye uku daga cikin jihohin 'yan kabilar Ndigbo amma munfukai irinsu Ekweremadu basu zauna da gwamnonin yankin sun bayyana kungiyar makiyayay a matsayin 'yan ta'adda ba kamar yadda suka yi wa kungiyar IPOB".
Kungiyar ta zargi Ekweremadu da hada baki da gwamnatin APC, da suka yi zargin ta Fulani ce, wajen cigaba da murkushe kungiyar IPOB ta kowacce hanya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng