Kalli yarinya ‘yar shekara 12 da ta wallafa littafi (Hoto)

Kalli yarinya ‘yar shekara 12 da ta wallafa littafi (Hoto)

Lois Chatta mai shekaru 12 a duniya ta rubuta wani littafin turanci wanda ta sanyawa suna, ‘Homeless at Home’ inda take kokarin jan hankalin al’umma game da tarbiyar ‘ya mace.

A cikin makon nan aka yi bikin kaddamar da littafi a Abuja wanda ya samu tantancewar Opanyi Samuel Oluwawumi.

Kalli yarinya ‘yar shekara 12 da ta wallafa littafi (Hoto)
Lois Chatta
Asali: Twitter

‘Homeless at Home’ an rubuta shi ne a kan wata yarinya ‘yar shekara tara mai suna Kaigama wadda iyayenta suka fita batunta saboda da namiji suke sha’awa ba mace ba.

Chatta ta ce ta rubuta wannan littafin ne saboda yadda ta ga ana nunawa diya mata halin ko in kula a wurare da dama. Wannan dalilin ne ya sanya ta rubuta littafin domin kawo sauyi cikin al’ummarmu, inji marubuciyar.

Chatta dalibar aji uku ne a karamar sakandare wato JSS 3, inda take zuwa makarantar Flora Home Academy, Abuja. Har ila yau ta bayyana mana cewa tana cigaba da rubuta wasu littafan domin kawo gyara ga al’ummarta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel