Coutinho ya bar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona

Coutinho ya bar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta tabbatar da bayar da Philippe Coutinho a matsayin aro zuwa ga kungiyar Bayern Munich ta Jamus.

Dan wasan wanda ya fito daga kasar Brazil ya gagara samun wurin zaman tun bara da komo kungiyarta Barcelona daga Liverpool.

KU KARANTA:Hajjin bana: Masari yayi kyautar kudi ga mahajjatan Katsina su 3,086

Kungiyar Barcelona tayita kokarin sayar da shi ga kulob din Ingila amma abin ya faskara, musamman yanzu da aka riga aka kulle cinikin ‘yan wasa a kasr ta Ingila.

A halin yanzu dai Coutinho zai koma kungiyar Bayern Munich dake Jamus, kamar yadda rahotanni da dama suka suna. Duk da cewa dai maganar ba ta kai karshe ba gaba daya amma dai anyi kusa saboda dan wasan bai cikin wadanda Barcelona ta tafi dasu Bilbao domin buga wasan farko a gasar La Liga ta bana.

Coutinho shi ne yake bugawa Barcelona lamba 11 sai ga shi kuma yanzu sun sayo Griezmann daga Atletico Madrid ga Dembele yana kulob din har yanzu.

Dadin dadawa kuma Barcelona na zawarcin tsohon dan wasanta Neymar wanda ke taka leda yanzu haka a kulob din PSG.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel